
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta koma cigaba shirye-shiryen da suka shafi kula da walwalar al’umma yayin da shirin ciyarwa ga ɗalibai zai cigaba da aiki da kuma raba kimanin Naira biliyan 493 ga magidanta.
Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin sake buɗe asusun Hukumar Kula da Shirin Walwalar Al’umma (NSIPA), wanda aka rufe tun a watan Janairun 2024 bisa zargin badaƙala.
Ministan Jin Ƙai, Dakta Yusuf Tanko Sununu ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja game da tasirin tallafin ƙasashen akan harkokin da suka shafi jin ƙai a Nijeriya.
Aƙalla ɗalibai miliyan tara ne suke karatu ba tare da samum ciyarwa ba sakamakon dakatar da shirin NHGSFP, lamarin da ya sanya ɗalibai da dama suka rage halartar makaranta.
