
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Gudanarwar Asibitin Nizamiye da ke Abuja ta ƙaryata batun da ke cewa jinkirin yin aiki ga marigayi Sanata Ibrahim Musa Kontagora sakamakon rashin kawo kuɗi akan lokaci ne ya yi sanadin rasuwarsa.
Ta ce, babu wani batun yi masa aiki da aka shirya yi a asibitin don haka ba ta da alhaki akan faruwar al’amarin.
Sanata Kontagora, wanda ya wakilci Jihar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa daga 2011 zuwa 2015, ya rasu ne a asibitin bayan shiga dogon suma na tsawon sama da sati guda.
Jami’in hulɗa da jama’a na asibitin, Mohammed Abubakar ya bayyana hakan yayin bada amsa ga a wani shafin yanar gizo da ke zargin gazawa wajen biyan Dala 30,000 na aiki ne ya yi sanadin mutuwar sanatan.
A wata hira da jami’in ta wayar tarho, ya ce asibitin ba ya aiki da Dala wajen karɓar kuɗi, sannan daga wani asibiti aka zo da shi zuwa nasu bayan fara yi masa jinya a can.
Ya kuma ce, babu shirn yi masa wani aiki a cikin abinda aka shirya yi masa a asibitinsu da ya shafi jinyarsa.
Sannan, ya yi watsi da batun cewa iyalan mamacin sun biya rabi kuɗin aiki, wato Dala 15,000 kamar yadda wasu kafafen labarai suka ruwaito.
