
Rundunar ƴan sanda ta saki ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi.
Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kirayen sakin nasa da aka yi.
Ya rubuta cewa, “Ƴan sandan Nijeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka an sake ni daga tsare ni da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.”
Saidai, ya ce babu wani abin farin ciki a sakin, “amma ina godiya gare ku da jajircewar da kuka yi ba tare da gajiyawa ba.”
Da fari, wasu matasa ne suka gudanar da zanga-zanga a Abuja da Legas da wasu birane, inda suka buƙaci ƴan sanda su sake shi ba tare da ɓata lokaci ba.
A ranar Laraba ne da ƴan sanda suka gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi, sannan rundunar ta sanar da cewa tana tsare da shi bayan ya ƙi amsa tambayoyi, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
