Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta cafke wasu masu kai saƙo guda uku da ake zargin su na raba haramtattun kayayyaki a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce, jami’an hukumar NDLEA sun gudanar da bincike a ƙarƙashin jagorancin sirri a yankunan Gwarimpa, Jahi, da Galadimawa a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Laraba 30 ga watan Yuli.
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin Sabo Sule mai shekaru 24; Samuel Nnamdi, mai shekaru 28; da Idris Jibrin, mai shekaru 28, ya ƙara da cewa an ƙwato jimillar kilogiram 149.8 na kwayar Canadian Loud, wani nau’in tabar wiwi mai ƙarfi daga gare su.
“Wasu mutane biyu da ake zargi, Aliyu Abubakar, 25, da Adekunle Agbabiaka, mai shekaru 30, an kama su ne a hanyar Abaji-Gwagwalada da kwayar skunk mai nauyin kilogiram 91.1, wani nau’in tabar wiwi a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta,” inji shi.
Babafemi ya ce, a Legas, jami’an hukumar NDLEA da ke aikin leƙen asiri a ranar Asabar sun kama wani Joseph Michael da kilogiram 3.3 na kwayar Colorado, wani nau’in tabar wiwi a Mushin.
Babafemi ya ƙara da cewa, an kama wani da ake zargin mai safarar miyagun ƙwayoyi, Ibrahim Sulaiman ne a unguwar Iwaya da ke Yaba ɗauke da lita 16.5 na kwayar skuchie a ranar Juma’a.
A cewarsa, an kama aƙalla kwayoyin maganin tramadol 100,000 daga hannun wani da ake zargi mai su na Hussein Yusuf, mai shekaru 37, a wani shingen binciken hukumar NDLEA da ke kan titin ɓandeikya-Ogoja a jihar Benue a ranar Juma’a.
Babafemi ya ce, a ranar da jami’an tsaro a jihar Edo suka kai samame a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Ekpoma, inda aka kama wani da ake zargi mai suna William Alabi, mai shekaru 44, sannan aka gano kwayar skunk mai nauyin kilogiram 233.5.
Ya ce, umarni da kafa hukumar a faɗin ƙasar nan sun ci gaba da yaƙi da shan muggan awayoyi, WADA, ayyukan wayar da kan makarantu, wuraren ibada, wuraren aiki da sauran al’umma a cikin makon da ya gabata.
Waɗannan sun haɗa da: Laccar faɗakarwa ta WADA ga ɗalibai da ma’aikatan makarantar Ciroma Ibrahim Islamiyya, Potiskum, Yobe; Sultan Maccido Institute for ƙur’an and General Studies, Wamakko, Sokoto.
Haka kuma an haɗa da direbobin katafaren motocin sufuri na Borno Eɗpress Serɓices, Maiduguri, jihar Borno; da masu ibada a cocin Seɓenth Day Adɓentist Church, Abakpa Nike, jihar Enugu.
Hukumar NDLEA ta jihar Osun ta kai ziyarar ban girma ga Oluwo na ƙasar Iwo Mai Martaba Sarkin Imperial Oba Abdurasheed Adewale Akanbi da dai sauransu.
