Manchester United ta kwashe fiye da shekara 10 ba ta yi wani kataɓus ba, idan aka kwatanta da yadda ta saba a baya, musamman lokacin da Sir Alex Ferguson yake horas da ‘yan wasan ƙungiyar.
Tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya a 2013 United ke neman kocin da ya dace da ita inda suka gwada irin su Jose Mourinho da Erik Ten Haag da David Moyes da Ralph Rangnick da sauran su, amma kowanensu ya gaza dawo da Manchester United kan ganiyarta duk da cewa wasu daga cikinsu sun lashe kofuna.
A watan Nuwamban 2024 ne Manchester United ta ɗauki Ruben Amorim a matsayin sabon mai horaswa domin maye gurbin Erik Ten Haag wanda ya shafe fiye da shekara biyu yana horar da ƙungiyar inda ya lashe kofin ƙalubale na FA a 2024.
Ruben Amorim ya koma Manchester United ne daga Sporting Lisbon inda a lokacin yake taka rawar gani a Portugal – ya lashe kufuna biyar cikin shekara huɗu, kuma salon wasansa ya riƙa ɗaukar hankalin masoya ƙwallon ƙafa.
Sai dai, tun bayan zuwan shi Manchester United wadda dama tana cikin garari, lamura suka fara taɓarɓarewa wa Amorim inda ya kafa wasu munanan tarihi.
Man United ta kammala kakar wasan 2024/2025 a matsayin ta 15 a teburin Premier League inda Amorim ya yi rashin nasara a wasanni 14, ya yi canjaras shida da nasara bakwai, hakan ya sa Amorim ne ke da kaso mafi ƙaranci a yawan makin da kowane kocin United ke samu a ƙarshen kaka tun bayan Alex Ferguson.
A gasar Europa League, United ta yi ƙoƙarin zuwa wasan ƙarshe amma Amorim ya gaza doke Tottenham a wasan, ba ta samu gurbin zuwa Champions league ba, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin magoya bayan Manchester United.
Baya ga abubuwan da ke faruwa cikin filin wasa, Amorim ya samu saɓani da wasu ‘yan wasan ƙungiyar da suka haɗa da Rashford da Garnacho inda ya zargi ‘yan wasan da rashin jajircewa a lokacin atisaye, kuma ya daina amfani da su a wasa.
Daga baya ‘yan wasan suka bayyana aniyarsu ta barin ƙungiyar inda wasu magoya bayan suka yi fushi da hakan, wasu kuma suka goyi bayan matakin.
Bayan kakarsa ta farko a Manchester United, akasarin magoya bayan ƙungiyar ba su da ƙwarin gwiwa saboda gaza taka rawar a zo a gani, amma duk da haka ƙungiyar ta ce tana goyon bayan Amorim kuma za ta ba shi goyon bayan da yake buƙata.
Zuwa yanzu, Manchester United ta sayi ’yan wasa biyu da suka haɗa da Matheus Cunha daga Wolverhampton Wonderers da Bryan Mbeumo daga Brentford.
Duk da cewa ƙungiyar ta ce tana cikin matsalar rashin kuɗi, ta kashe fiye da fam miliyan 130 kan ‘yan wasan biyu kuma tana zawarcin Benjamin Sesko.
Rahotanni sun kuma ce United na neman sabon mai tsaron raga da ɗan wasan tsakiya.
Duk da haka, United ta lashe gasar wasannin share fage na wasu ƙungiyoyin Premier League da aka gudanar a nahiyar Asiya inda sabbin ‘yan wasan biyu Cunha da Mbeumo suka fara taka wa ƙungiyar leda.
Mai sharhi kan wasanni Simon Stone ya ce Manchester United ɗin da ta lashe wannan gasar sabuwa ce.
“Da alama wannan Manchester United ɗin sabuwa ce. ‘Yan wasan sun fara fahimtar salon wasan Amorim,” inji Simon.
