
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama wani mai suna Taufiq a Unguwar Sabuwar Gandu da ke jihar bisa zarginsa da hannu a ayyukan da suka shafi bokanci.
Mataimakin Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudden ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Juma’a, inda ya ce al’amarin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’ummar yankin suka yi ta kai wa jami’ansu.
Ya ce, bayan mazuana unguwar sun koka ne hukumar ta gaggauta gudanar da bincike, lamarin da ya sa aka kama shi.
Ya kuma ce, za a maka shi a kotu bisa zargin sa da aikata laifin, wanda ya saɓa wa dokokin jihar.
