Peter Obi na son a mayar da wa’adin mulkin shugaban ƙasa shekara biyar zango ɗaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi kira da a mayar da zangon mulkin shugaban ƙasa shekara biyar da soke tsarin yin zango biyu.

Da ya ke magana yayin wata ziyara ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed a ranar Juma’a, Obi ya ce yin hakan zai taimaka wa jagorori wajen mayar da hankali ga harkokin shugabanci madadin shirin sake neman zaɓe.

Ya bayyana cewa, a tsarin da ake tafiya a yanzu, shugabanni suna ɓata lokaci mai muhimmanci wajen mayar da hankali akan samun nasara a karo na biyu, wanda yin hakan na haifar wa sauke nauye-nauyuensu tsaiko.

Game da zaɓen 2027, Obi ya yi alƙawarin cewa matuƙar aka zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya, wa’adin mulki ɗaya kacal zai yi kuma ba zai cigaba da riƙe muƙamin ba sama da shekaru huɗu ba.

Ya kuma yi nuni da muhimmancin ƙarfafa jam’iyyun siyasa ta yadda za su samu ƙarfi sama da ɗaiɗaikun jami’an gwamnati kamar su shugabannin ƙasa da gwamnoni domin kiyaye dokoki.

A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga Obi da ya koma cikin jam’iyyar PDP domin a cigaba da damawa da shi, yana mai cewa suna da kyakkyawan shiri akansa.

Haka kuma ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su ajiye soye-soyen zuciyarsu da haɗewa wajen yin aiki tare don ciyar da Nijeriya gaba.

By Babaji