Gwamna Raɗɗa ya bi sahun al’ummomi wajen sauraren buƙatun al’umma na kasafin kuɗin 2026

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An gudanar da sauraron jama’a kan buƙatar su da zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen tsara kasafin kuɗin 2026.

Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya ƙirƙiro da wannan tsari kuma ya umurci zaɓaɓɓun wakilai da masu riƙe da muƙamin siyasa da suje mazaɓun su jagoranci sauraron al’ummar su.

Malam Dikko Raɗɗa ya gana da al’ummar mazaɓar sa ta Raɗɗa, da ke ƙaramar hukumar Charanchi, a wajen taron shirin tattara muhimman buƙatun al’umma da za a sanya a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Taron wanda Gwamnan ya halarta ta yanar gizo na matsayin wani mataki na bin sahun sauran al’ummomin mazaɓu 361 da ake da su a faɗin jihar, inda mahalarta taron a mazaɓar Raɗɗa su ka samu damar bayyana manyan buƙatun su, tare da samun amsoshin su kai tsaye daga gwamnan jihar.

Kamar yadda ya bayyana a jawabin da ya gabatar wa al’umma~ “Mun zo ne anan domin mu saurari Koken ku, ya zama wajibin mu, mu faɗa wa kan mu gaskiya, duk wani cigaba ana samar da shi ne tun daga tushe.

Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada cewa, wannan shiri na da aka shirya a matakin mazaɓu ya bambanta da tsohuwar hanyar tsara kasafin kuɗi, ya na mai cewa, ” Mun zo ne domin ba ku damar bayyana buƙatun da kuke da su da kawunan ku, ba wai mu zauna daga ofisoshi mu tsara wa al’umma abun da suke bukata ba, kuma wannan mataki shine hanya ɗaya tilo da za a iya aiwatar da Kasafin kuɗin da ya dai-dai da buƙatun al’umma “.

Haka kuma, a lokacin taron Gwamna Raɗɗa ya yi cikakken bayani akan cewa, a lokaci guda gwamnati ba za ta iya aiwatar da dukkanin buƙatun da al’umma suka gabatar ba, sai dai da sannu a hankali gwamnati za ta riƙa gudanar da muhimman ayyukan da ko wace mazaɓa ke da su.

Ya bai wa al’umma tabbacin tattara dukkanin buƙatun da suka gabatar, tare da hannanta su ga ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta jiha, da kuma hukumar kula da shirin cigaban rayuwar al’umma (CDP), domin ganin an sanya su a cikin jerin kasafin kuɗin da za’a gudanar.

Kamar yadda ya ce, “Mun zo ne domin yin kyakkyawan tsarin da zamu samarwa kawunan mu cigaba, don haka mu sani wannan shiri ba siyasa ba ne, kuma da hakan ake shimfida kyakkyawan Shugabanci nagari ga al’umma”.

Gwamnan ya yabawa al’ummar yankin bisa ga gudummawar da su ka bada, tare da shan alwashin gwamnatin sa na cigaba da sauraren Koken al’umma, da kuma kamanta adalci, da gaskiya.

Taron ya samu halartar masu riƙe da sarautun gargajiya, da ƙungiyoyin matasa, da na mata, da kuma nanoma, tare da malaman makarantu, da sauran masu ruwa da tsaki na al’umma.

A wani makamancin wannan kuwa, an gudanar da tarukan jin ra’ayoyin al’ummar a dukkanin ƙananan hukumomi 34 dake Jihar Katsina, domin tabbatar da shigar al’umma a cikin tsarin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Jihar Katsina Ibrahim kaula Muhammad.

By ukarofi