Gwamna Abba ya kori mataimakansa biyu bisa hannu a belin dillalin ƙwaya da sauya akalar tallafi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar manyan mataimakansa guda biyu bayan kwamitin bincike ya gano suna da hannu a aikata wasu laifuka.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya bayyana haka a wata sanarwa, ranar Asabar.

A cewar Sakataren, an tsige Abubakar Umar Sharaɗa, wato mai taimaka wa gwamnan kan wayar da kan al’umma akan harkar siyasa bayan gano yana hannu a belin dillalin ƙwayan nan Sulaiman Ɗanwawu, kamar yadda hadimin ya tabbatar wa kansa laifin.

A ɗaya gefen, an sallami Tasiu Adamu Al-amin Roba, wato mai taimaka wa a ofishin ma’aikatan gwamna sakamakon kama shi da laifin ɓoye kayan tallafi a wani rumbu da ke unguwar Sharaɗa.

Akan haka ne aka umarci jami’an biyu da su dawo da baki ɗaya kayayyakin gwamnati da ke hannunsu daga yanzu zuwa ranar 11 ga Agusta, 2025.

Haka kuma, gwmnan ya wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai taimaka masa akan harkokin magudanan ruwa bayan kwamitin bincike ya gano cewa ba shi hannu a baki ɗaya laifukan da ake tuhumar sa a kansu.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci yayin gudanar da harkokin gwamnatinsa.

By Babaji