
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
John Utaka, wanda tsohon ɗan wasan gaba ne na Super Eagles, ya zama sabon mai horar da ƴan wasa mata na ƙungiyar Montpellier HSC bayan maye gurbin Frederic Mendy.
Utaka zai yi aiki ne tare da Baptiste Merle zuwa ƙarshen wannan kakar a ƙarƙashin kulawar Daraktan wasanni na ƙungiyar, Jean-Louis Saez.
Lamarin da ya tsohon ɗan wasan ya zama ɗan Afirka na farko da ke jagorantar tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata da ke cikin babar gasa a Faransa.
Gabannin ya yi murabus, Utaka mai shekaru 43 ya taimaka wa tawagar maza ta ƙungiyar nasarar lashe kofin League 1 a kakar 2011/2012, inda ya zura ƙwallaye biyu a wasan ƙarshe da ya bai wa ƙungiyar nasarar lashe kofin a karon farko a tarihinta.
Ya kuma dawo a matsayin kocin ƴan wasan gaba na matasa a ƙungiyar a shekarar 2020, sannan kuma ya jagorancin ɓangaren matansu a 2021 na ɗan lokaci.
Magoya bayan ƙungiyar za su kasance cikin zaƙuwa wajen ganin Utaka, wanda haifaffen Enugu ne ya sake dawowa domin cigaba da bada gudunmuwarsa a gare ta.
