Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Iyayen ɗaliban Jihar Zamfara kimanin su 88 da har yanzu suke maƙale a jami’ar ƙasar Cyprus International University sun roƙi gwamnan jihar Dauda Lawal da ya kawo ɗauki cikin gaggawa domin warware basussukan da ake bin cibiyoyin ilimin su a ƙasar Cyprus na sama da Naira Biliyan ɗaya.
A wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Asabar, shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban Cyprus, Ibrahim Tudu, ya ce ɗaliban na fama da matsananciyar wahala, tare da ƙarewar takardar izinin zama, da rashin biyan kuɗin karatu, da kuma rashin masauki.
“Har yanzu muna kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya warware basussukan da ake bin wadannan ɗaliban domin ‘ya’yanmu su ci gaba da karatu a matakai daban-daban da kuma fannoni daban-daban,” in ji Tudu.
Ya bayyana cewa an ta yaɗa labaran ƙarya game da halin da ɗaliban ke ciki, inda ya jaddada cewa bashin da ake bin ya haura biliyan ɗaya.
“Har yanzu ba a biya duk kuɗin makaranta, masauki, izinin zama, da alawus alawus na ciyarwa ba ga ɗaliban”. Inji shi
Ya ƙara da cewa “Muna sake yin kira ga mai girma gwamna da ya ɗauki matakin gaggawa don biyan waɗannan basussuka.”
Sai dai a kwanakin baya babban mataimaki na musamman ga gwamna, Malam Mustafa Jafaru-Kaura ya bayyana cewa tuni gwamnati ta biya Naira miliyan 290 domin kula da ɗaliban.
Ya kuma yi ikirarin cewa an ba su tikitin jirgi don komawa Najeriya, amma sun ƙi dawowa.
