
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake cigaba da kusanto rufe yin rajistar amfani da gilashi mai duhu ga masu ababen hawa, rundunar ƴan sanda ta yi shuru akan fitar da bayanan matakan da aka shirya wa akan batun, lamarin da ya jefa su cikin duhu.
An fara rajistar ne a ranar a ga watan Mayu, 2025 a lokacin da rundunar ƴan sandan ta buɗe ƙofar yin rajista ta yanar gizo ta izinin amfani da gilashin duba da yadda ake tsangwamar masu ababen hawa akan mallakar irinsa.
Rundunar ta ce, ta fito da tsarin ne don tabbatar da tsayar da gaskiya da adalci da inganta harkar tsaro musamman wajen rage aikata manyan laifuka a Nijeriya.
Akan haka ne da fari ta bada wa’adin wata guda domin bai wa masu ababen hawan damar yin rajistar, inda daga bisani aka ƙara wa’adin zuwa 12 ga Agusta, 2025.
Rashin fitar da sabon jawabi kan al’amarin duba da saura kwana biyu ya haifar da fargaba acikin jama’ar.
