Daga JOHN D WADA a Lafiya
Kimanin ‘yan gidan gyara hali 16 ne suka tsere daga gidan gyaran hali da ke garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa a yau Talata 12 ga watan Agustan shekarar 2025 da ake ciki.
Lamarin yayi sanadiyar samun munanan raunuka da wasu jami’ai dake kula da gidan yarin su biyu suka samu.
Tuni mahukuntar gidan yarin suka tabbatar da aukuwar lamarin inda suka bayyana cewa jami’ai biyun da suka samu munanan raunin a yanzu haka suna samun kulawar likitoti a wani asibitin gwamnati.
Mai magana da yawun gidan yarin, Abubakar Umar ya sanar wa manema labarai ciki har da wakilin mu cewa a yanzu haka an cafke mutum 7 daga cikin waɗanda suka tsere yayin da jami’an hukumar tare da haɗin gwiwar sauran jami’oin tsaron daban daban na cigaba da sintiri na musamman don sake kamo sauran tara da suka rage.
A nasa ɓangaren kwanturola janar na hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche wanda ya ziyarci inda lamarin ya auku don gane wa idanun sa ya umurci a gudanar da cikakken binciken gaggawa a kan lamarin kana ya sha alwashin sa ƙafar wando guda da duk jami’in hukumar da binciken ya gano yana da hannu ciki aukuwar mumuman lamarin.
Yace ” wannan babban bala’i ne shiyasa muke gaggawar gano musabbabin sa da kuma waɗanda zai iya yiyuwa an haɗa baki dasu daga cikin jami’an mu.
Kare lafiyar ƴan Najeriya shine babban burin mu a ko yaushe.” Inji shi.
A ƙarshe sai kwanturola janar ɗin ya buƙaci al’umma baki daya su kasance da lura sannan su tabbatar sun kai ƙara ko rahoton duk wanda basu gamsu da shi ba zuwa ofishoshin jami’an tsaro mafi kusa.
