Wararrun ‘yan majalisar dokokin Zamfara sun yi Allah wadai da gwamnatin jihar kan matsalar tsaro

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wararrun ƴan majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Rt Hon Bashar Aliyu Gummi ta sake yin Allah wadai da halin ko in kula da Gwamna Dauda Lawal Dare ke yi kan matsalar tsaro a jihar.

‘Yan Majalisar sunyi kira ga gwamnatin tarayya da ta haɗa kai da jami’an tsaro a Zamfara domin ceto rayukan al’ummar jihar da dukiyoyinsu kamar yadda yake ƙunshe a kundin tsarin mulki Kashi na biyu.

A zaman su na yau, ‘yan majalisar sun yi nasu bitar yadda ‘yan bindiga suka lalata jihar ta hanyar kai hare-hare a wasu al’ummomi da dama a faɗin jihar.

Sun koka kan yadda gwamnan da gwamnatinsa suka fi nuna damuwa kan takararsa a karo na biyu maimakon mai da hankali wajen ceton alummar jihar daga hare-haren ‘yanbidiga .

Mambobin waɗanda suka caccaki gwamnan da cewa bai taɓa kai ziyarar jaje ba ko tura tawagar gwamnati ko agaji ga al’ummomin da abin ya shafa ko iyalan waɗanda abin ya shafa, sun yi nuni da cewa kwatsam gwamnan ya gane cewa zai buƙaci goyon bayan al’ummar ƙaramar hukumar Kaura Namoda don samun nasara a zaɓen majalisar dokokin jihar da za a yi a ƙarshen mako mai zuwa, tare da cewa a halin yanzu yana shirin jajanta wa al’ummar Banga da ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Da yake gabatar da ƙudiri kan lamarin, Honarabul Bashir Abubakar Masama, mamba mai wakiltar Bukkuyum ta Arewa, ya yabawa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na yaƙar ‘yan bindigar duk da yadda gwamnatin jihar ke ci gaba da ɓatawa jami’an tsaro rai.

Ya ce a yankinsa kaɗai al’ummomin ƙauyuka huɗu da suka haɗa da Adapka, Zauma, Gwashi da Mayanchi da ke kan hanyar Bukkuyum sun fi shan wahala a hannun yan ta’addan.

Da yake goyon bayan ƙudirin, Honarabul Bashir Bello Sarkin Zango mai wakiltar Bungudu ta Yamma, ya ƙara da cewa a ƙaramar hukumarsa, Gidan Bugaje, Zaman Gida, Kukan Nine da Gidan Dan-inna, gungun miyagu sun raba alummar yankin da garuruwan su, inda duk wanda ya kuskura ya je ana kallonsa a matsayin mai ƙararren kwana.

‘Yan majalisar yayin da suke bayyana damuwarsu da rashin jin daɗin su ga gwamnatin jihar sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta samar da cikakken iko akan lamarin tsaro a jihar.

“Idan har gwamnatin tarayya ta yi watsi da yadda gwamnatin jihar keyin zagon ƙasa ga jami’an tsaro, za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da ‘yan bindigar. Suka ba da shawara

‘Yan majalisar sun yi kira ga al’ummar Zamfara da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda tare da baiwa jami’an tsaro sahihin bayanai kan duk wani mutane da ake zargi da aikata laifuka domin a kama su kafin su aikata wani laifi.

By ukarofi