Daga JOHN D. WADA, a Lafiya
Sanata wanda ke wakiltar shiyar Nasarawa ta Gabas da ke Jihar Nasarawa a majalisar dattawa ta ƙasa, Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya canja sheka daga tsohuwar jam’iyyar sa ta SDP zuwa ta APC mai ci a jihar sa ta Nasarawa bayan wani ganawa na musamman da yayi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasar da ke birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Talata. Ya bayyana kan sa a matsayin cikakken ɗan sabuwar jam’iyyar APC ɗin duk da bai canja shekar a hukumance ko ba.
A cewar sanata Aliyu Ahmed Wadada da yake jawabi da manema labarai jim kaɗan bayan ganawar nasa da shugaba Tinubu yace a yanzu kam babu wani ko wata daga cikin duka jam’iyyun adawa a ƙasar nan da zai iya karawa da Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 don babu wanda ya taba yi abubuwa da yayi a matsayin shugaban ƙasa da kuma lokacin da yake gwamnan Legas kuma baza a iya yin kamar sa ba.
Sanatan da ya canza shekar ya ƙara da cewa kawo yanzu tuni bincike ya kuma tabbatar cewar galibin ‘yan Najeriya suna maraba da murnar salon shugabancin shugaban ƙasar kuma baza su bai wa jam’iyyun adawa damar ƙalubalantar haifaffan ɗan birnin Legas din ba inda ya ƙara da cewa babu mai farin-jini gun al’umma kamar sa a cikin duka ‘yan takaran.
Sanata mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Gabas ɗin, Sanata Aliyu Ahmed Wadada daga nan sai yayi amfani da damar inda ya godewa shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da karramawa da yake yi masa tun ma kafin ya canza shekar inda ya bai da misali yadda a ‘yan kwanakin baya nan ma duk da yana tsohuwar jam’iyyar nasa na SDP shugaba Tinubun ya turo babban sakataren gwamnatin tarayya wato Cif George Akume ya wakilce shi da sauran manyan muƙarraban gwamnatin sa na tarayyar a wani wajen babban bikin naɗin sarautar gargajiya na ƙasa da ake kira (Magajin-Dengi) da akayi masa a fadar mai martaba sarkin Lafiya birnin Lafiya a Jihar ta Nasarawa da sauran karramawa da soyayya da yake nuna masa akai-akai kafin ma yanzu kenan inji shi.
Canja shekar da shi Sanata Wadada yayin wakilin mu a Jihar ta Nasarawa dai ya lura cewa hakan ya faru ne bayan ‘yan kwanaki kaɗan kawai da babban sakataren sabuwar jam’iyyar nan ta adawa ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola ya ziyarci yankin na shiyar Gabas inda ya gana da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa don nemo hanyoyin ƙwace ragamar mulkin ƙasa daga gun shugaba Tinubu da sauran madafan iko na siyasa a duka jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar nan baki ɗaya a zaɓukan gama-gari na 2027 ɗin da ke tafe.
