Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Idan ka ji an ce ga wata Indian Girl, mai yiwuwa tunaninka ya ta fi zuwa ƙasar Indiya, ko kuma ka fara tunanin ganin wata yarinya ýar ƙasar Indiya. To, wannan Indian Girl ɗin ta marubuta ce, kuma ýar Nijeriya daga Jihar Kano. Tana daga cikin matasan marubutan onlayin masu baje ilimi da basira a zaurukan marubuta na WhatsApp da Facebook, inda take fitar da labarai da suka shafi soyayya da zamantakewa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Indian Girl, wacce asalin sunanta shi ne Zainab Muhammad ta bayyana yadda aka yi ta samu wannan suna da gudunmawar ta a harkar rubutun adabi.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
ZAINAB: Sunana Zainab Muhammad wacce aka fi sani da Indian Girl. Ni marubuciya ce, kuma ina sana’o’in hannu kala-kala. Amma babbar sana’ar hannu da nake ji da ita, ita ce rubutu, wanda nake jinsa a jini da jijiyata, kuma nake alfahari da shi. Ni ba matar aure ba ce, amma ina fatan kasancewa amarya, nan da ɗan wani lokaci.
Zan so ki bamu tarihin rayuwarki.
Ni haifaffiyar garin Kano ce, daga ƙaramar Hukumar Dala, a unguwa mai suna Ayagi, da ke kusa da asibitin Jakara. An haife ni a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2003. Na yi karatuna tun daga matakin makarantar rainon yara, (Nursery) har zuwa sakandire. Bayan na yi nasara da kyakkyawan sakamako, na fara karatun NCE na ɗan wani lokaci kafin wasu dalilai su sa na tsaya. Kodayake har yanzu ba wai na bari gaba ɗaya ba ne, in sha Allahu zan cigaba nan ba da darewa ba, don ina da burin karatu mai zurfi sosai. Na yi karatun Islamiyya a wata makaranta mai suna Sahatus-Subyan Ayagi, bayan ita kuma na yi makarantar allo da ake kira Mai Jalingo. Ilimin addini dai daidai gwargwado na samu. Alhamdulillah.
Me ya sa ake miki laƙabi da Indian Girl?
A onlayin ne na samu suna da ake min laƙabi da shi na Indian Girl, lokacin ban jima sosai da kasancewa marubuciya ba. A lokacin muna da wani zaure na marubuta ƙarƙashin ƙungiyar mu, a manhajar WhatsApp sai mambobin zauren suka riƙa sanyawa kansu laƙabobi na basaja, da kowa yake so a riƙa kiran sa da shi, don a yi raha a yi dariya. Shi ne nima na saka nawa sunan Shalelen Nobel, kasancewata ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar. Daga baya kuma na yi amfani da sunayen irin su Zee Pretty, sannan na dawo Mrs. Ramcharam, daga baya shi ne kuma na saka India Girl, wanda a sannan da wasa ne na yi hakan muke dariya, amma sai sunan ya zama laƙabin da ya bi ni. Har ma da yawa ba sa sanin asalin sunana, Zainab Muhammad, sai dai Indian Girl. Na so sauya sunan amma hakan bai samu ba, domin kafin na sauya a sanni da shi zai yi wuya.
Wacce irin rayuwa ki ka yi lokacin tasowarki da gwagwarmayar da ki ka sha, kawo yanzu?
To, Alhamdulillahi. Ni dai Allah Ya ƙaddara rayuwata na taso a gida mai tarbiyya daidai gwargwado, kuma ana zumunci da juna sosai, a yi wasa da dariya yadda ya kamata. Kasancewar na taso ne a babban gida, wato gidan gado inda kowa ke zaune a sashin sa tare da iyalinsa. Amma duk da haka akwai tarbiyya da tsawatarwa, babu takurawa, amma kuma ba a barin shashanci da zubar da mutunci. Ina aji shida na makarantar firamare, lokacin za mu yi jarrabawar tafiya sakandire babana ya rasu, bayan rasuwarsa mun cigaba da kansacewa a ƙarƙashin kulawar dangin mahaifinmu.
Kina daga cikin matasan marubuta na onlayin, ko za ki gaya mana yadda aka yi ki ka zama marubuciya?
Tun lokacin da muka shiga makarantar sakandire nake yawan karatun littafi, wanda idan na sayo na ɗaya zuwa huɗu ko zan kai asuba sai na gama karantawa sannan nake barci. A lokacin sallah ce kawai take tashina daga karatun ko aiki ba na yi. Hakan ya sa aka riƙa yi min barazanar ƙona littafin idan ban daina karatun ba. Amma da yake na yi nisa ban fasa ba, amma sai nake ɓoye shi a littafi kamar mai karatun makaranta, har zuwa shekara ta 2021 a lokacin muna shirye-shiryen fita daga sakandire. A sannan ne na samu babbar waya, wacce a kanta ne na buɗe Facebook.
A dalilin yawan amfani da facebook da nake yi ne watarana sai na karanta rubutun wani marubuci ana ce masa Haruna Birniwa, wanda ya yi akan masu sha’awar rubutu. Bayan na ga wannan rubutun ne sai na ji ina da sha’awar hakan, sai na yi masa magana har ya fara ɗora ni a hanya. Da haka har na fara gwada rubutun kaina, yana nuna min hanya. Bayan nan kuma sai na haɗu da wata marubuciya Ameesha MD, wacce ita ma ta cigaba da ɗora ni a hanya kafin haɗuwa ta da ɗeryyishertul-Humaira inda na nuna sha’awar na shiga ƙungiyarta ta Nobel Writers Association. Daga nan ne kuma na daɗa sanin wasu marubutan sosai.
Dama ina so in miki tambayar ko waye ya fara nuna miki yadda ya kamata ki yi rubutun labari?
E, kamar yadda na faɗa, marubuci Haruna Birniwa shi ne wanda ya fara nuna min hanyar da zan bi na zama marubuciya da kuma yadda rubutun adabi yake.
Shin kina karanta littattafan wasu marubutan? Kuma wanne littafin ki ke karantawa a halin yanzu?
E, tabbas ina karanta littattafan wasu marubutan sosai ma kuwa, duk da dai yanzu ban cika karatu kamar da ba. A halin yanzu littafin da nake karantawa shi ne littafin da marubuciya Na’ima Sulaiman Sarauta (Nimcyluɓ) ta rubuta mai suna ‘Uncle Ne’.
Wacce marubuciya ko marubuci ne allon kwaikwayonki, ko wacce salon rubutunta ya fara sa miki sha’awar rubutu?
Marubutan da nake kwaikwayo suna da yawa gaskiya, kuma ina matuƙar jin daɗin salonsu, akwai irin su Anti Bilkisu H. Muhammad, sannan kuma akwai Anti Fauziyya D. Sulaiman, sai Anti Nazeefa Sabo Nashe. Gaskiya waɗannan marubuta ukun da na ambata su ne allon kwaikwayona. Har yanzu ba na mantawa da littafin Anti Bilkisu mai suna ‘Dake Na Dace’, da littafin Anti Fauziyya mai suna ‘Daren Baƙin Ciki’, sai na Anti Nazeefa mai suna Gaskiyar Lamari. Akwai littattafai da dama da suka sa min sha’awar rubutun su, kuma na ji suna burgeni sosai. Kodayake ba za a rasa wasu littattafan ba, waɗanda na ji daɗin karatun su, amma kuma na manta sunan marubutan.
Kawo yanzu littattafan ki nawa, kawo sunayen su?
Kawo yanzu na rubuta littattafai kamar 12, sannan akwai waɗanda ban kammala ba. A cikin su akwai ‘Wani Gida’ (Gidan Gado), ‘Yayi Ne’, ‘Abeesa Ko Ameesha’, ‘Matar Mijina’, ‘Matar Mijina’ (Return), ‘Sanadiyyarta,’ ‘Wacece Ni?’ ‘Uwar Miji Ko Kishiya’, ‘Ba Don Ina So Ba’, ‘Bana Ra’ayi’, ‘Matar Abokina’, sai kuma, ‘Rayuwar Anoosha’.
Ki yi mana bitar darussan da wasu daga cikin littattafanki suke koyarwa?
Littafin, ‘Uwar Miji Ko Kishiya’, Labari ne da ke koyar da darasi akan haƙuri da juriya. Yarda da ƙaddara, kai wa Allah kukan ka, da yarda da shi akan Zai amsa maka, Yana jinka da ganinka.
Shi kuma littafin, ‘Sanadiyyarta’, yana ɗauke da darasi ne akan illar rashin kunya, rashin ji da ƙiriniya, rashin girmama babba, da rashin jin maganar iyaye.
Yayin da littafin ‘Rayuwar Anoosha’ yake koyar da darussan da suka shafi, iyaye su daina takurawa ‘ya’yansu akan rashin samun miji, haƙuri da ƙaddara, juriya, addu’a, da sauran darussa daban-daban.
Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu akai, kuma wanne lokaci ne ki ka jin daɗin yin rubutu?
A gaskiya ni kowanne lokaci na ji ina da sha’awar rubutu, ko na rubuta labari wanda zai tafi akan abu kaza sai na rubuta. Wani lokacin kuwa sunan labari ne ke bani jigonsa. Idan ya zamana na samu sunan labari to, na kan samu jigo ta hanyar sunan. Ni kowanne lokaci ina iya yin rubutu, idan har a raina na ji hakan kawai zan yi. Amma idan ba na son yi ko na yi shirin farawa, sai na ji na kasa dole na haƙura.
Wanne alheri ki ka taɓa samu a dalilin rubutu?
To, Alhamdulillahi. Akwai alkhairai da dama da zan ce na samu. Ka ga dai akwai sanin waɗanda mutum bai yi tunanin sani ba. Akwai mutumtaka, don mutumtaka ma alheri ce babba. Sannan kuma na taɓa samun wani alheri ta hanyar wata gasa da na shiga wadda jaridar Leadership Hausa ta saka akan rubutun Gajeren Labari na soyayya a shekarar 2024. Na yi nasarar shiga gasar inda na yi sa’a na zo ta biyu a gasar, da labarina mai suna, ‘So Sila,’ wanda ban taɓa tsammanin samu ba. Sannan akwai wasu wanda zaurukan marubuta ke sakawa, nan ma na yi nasara. Duk wannan alheri ne daga Ubangiji. Alhamdulillah.
Yaya ki ke sanin labarinki yana samun karɓuwa a wajen masu karatu?
To, a gaskiya idan labari ya karɓu za a riƙa bi na har ta shafina ana tambaya ta, idan ba a ga na fitar da labari ba. Wani lokacin kuwa ba a ma cewa komai, sai lokacin da ba a tura labari ba za a yi ta nema. A nan ne zan gane ashe ana so maganar ce dai ta zama aiki.
Ta yaya ki ke mu’amala da masu bibiyar littattafan ki?
Gaskiya, Alhamdulillah. Ina iya ƙoƙarina wajen ganin an yi wasa da dariya an yabi juna, ba na son a riƙa gulma ta ana cewa wane ai ya fiye yin kaza da kaza. Gaskiya na fi son faran-faran da mutane.
Bayan rubutu akwai wata harka da ki ke yi ne, ta sana’a ko kasuwanci?
Ba na sana’a ta musamman, sai dai ‘yan ƙananan sana’o’in hannu waɗanda ake sarrafawa, kamar aikin ɗinkin hula kamar su zanna da sauransu.
Bayan baiwar rubutu, wacce basira ki ke da ita wanda ba kowa ya sani ba?
Ba a rasa ɗan’adam da baiwa kala-kala, wasu sun bayyana ya sani, wasu kuma bai sani ba. Ina da baiwa ta saurin fahimtar ɗan’adam da karantar me ke tattare da shi.
Wanne salon labari ki ka fi son rubutawa, soyayya, almara, ko zamantakewa?
Salon da na fi son rubutu akai shi ne soyayya, sai kuma zamantakewa.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako take miki a harkar rubutun adabi da ki ke yi?
A halin yanzu ina cikin sabuwar ƙungiya ne mai sunan Farinwata Writers Association. Kuma tana taimakona daidai gwargwado, musamman kasancewar jajjirtacciya ce ta kasance shugaba a gareta.
Wanne ƙalubale ki ke ganin ya fi damun marubuta a wannan lokaci, wanda ya kamata su gyara?
Nuna fifiko, da nuna wancan na fi sani wancan ne ban san shi ba. Marubuta da dama muna nuna cewa don ba mu san wane ba, ba za mu yi tarayya da shi ba, ba za mu zama tamkar ɗaya da shi ba. Sannan ba za mu yi hira da shi ba. Sau da dama sabbin marubuta da kuma wasunmu a cikin marubuta suna jin ba daɗi game da wariyar da ake nunawa tsakanin waɗanda ake iƙirari da tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Sannan mu rage nuna ɗagawa da girman kai, ga baiwar da Allah ne ke ba da ita ba bawa ba. Don wane ya zo ya ce ina son zama marubuci ka nuna masa hanya, ba ka nuna masa cewa baiwar rubutu fa ba tasa ba ce da zai shigo ta da ka ya yi mata katsalandan. Yakamata mu riƙa taimakawa juna duk ta inda ƙarfinka ya fi. Taimako dai taimako ne, ko da ba da kuɗi ba, idan ka taimakawa wani Allah zai dube ka kai ma ya taimake ka. Sannan duk da rubutun batsa ya ɗan ragu a duniyar rubutu amma mu dage mu cire shi gabaɗaya daga fannin basirarmu mu ɗauki daidai mu rubuta, domin duk abinda muka rubuta Allah Subhanahu Wa Ta’ala, sai ya tambaye mu. Mu aikata abin da ya kamata sai Allah ya sa da mu dace, ameen.
Idan kin samu dama wanne gyara za ki so ki kawo don cigaban rayuwar mata da marubuta ýan’uwanki?
Tabbas idan na samu dama zan taimaki marubuta ta hanyar ɗaga darajar su. Na nuna wa duniya cewa marubuta ginshiƙi ne, kuma jigo ne ga rayuwa. Zan ɗaukaka, su zan inganta su zan wadata su ta yadda za su dinga alfahari da kasancewarsu marubuta. Mata kuma zan nuna musu cewa su ma fa suna da dama da ‘yanci na gina rayuwarsu da kawo sauyi da gyara a rayuwar al’umma bakiɗaya mata masu daraja ne a ko ina suke.
Wanne buri ki ke da shi nan gaba a rayuwarki?
Ina da burin ganin na ɗaukaka a duniya, an san da ni sosai. Sannan ko’ina na shiga a nuna ni a ce ga marubuciya wance. Ina da burin ganin na kawo sauye-sauye iri-iri a cikin al’umma ta sanadin rubutu.
Wanne karin magana ne ya fi ɗaukar hankalinki?
Gida biyu maganin gobara. Wato, idan wannan hanya ta toshe, sai ka ɓulle ta waccan. ƙarin magana ne mai ma’ana sosai.
