Magoya bayan Ɗankwambo na akwatin zaɓe sun sauya sheka zuwa APC a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A wani muhimmin sauyin siyasa da ya auku a Jihar Gombe, magoya bayan akwatin rumfar zaɓen tsohon Gwamnan Gombe, Dakta Ibrahim Hassan Ɗankwambo, sun sauya sheka daga jam’iyyar su ta PDP zuwa jam’iyyar APC.

Shugaban ƙungiyar shugabanin ƙananan hukumomi na Gombe wanda shi ne shugaban ƙaramar hukumar Gombe Barista Sani Ahmad Haruna , shi ne ya karɓe su a wani biki da ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa da magoya baya daga tushe.

Wannan sauyin sheka, wanda hadimin gwamna na musamman kan harkokin GOSTEC, D.J. Mai Taya, ya jagoranta, ya haɗa da ɗimbin tsofaffin mambobin jam’iyyar PDP da suka yi alƙawarin yin biyayya ga jam’iyyar mai mulki.

Yayin taron, Barista Sani Haruna ya yabawa sabon matakin da suka ɗauka, yana mai tabbatar musu da daidaito a tsakanin su da tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka jima a cikin ta.

DJ Mai Taya ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar kowa, wacce ke kishin kawo haɗin kai, ingantaccen shugabanci da ci gaba mai ɗorewa a fadin jihar.

Da yake jawabi a madadin Shugaban APC na jiha, Nite K. Amangal, Shugaban APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, jinjinawa haɗin kai ya yi na tsakanin mambobin jam’iyyar, tare da yin alƙawarin ci gaba da tallafa wa dukkan mambobi tsofaffi da sababbi.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan sha’anin tsaro, Abubakar Aminu Musa ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar nasara a wajen ƙarfafa haɗin kan siyasa da kuma faɗaɗa damar shiga jama’a cikin sha’anin mulki daga tushe.

A cikin jawaban su daban-daban, wasu daga cikin sababbin mambobin sun bayyana gamsuwar su da salon shugabancin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da yabawa nasarorin ci gaba da APC ta samu a matakin jiha da na ƙasa, suna mai cewa hakan ne ya fi jawo hankallin su zuwa jam’iyyar APC.

Taron, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyya, kansiloli da magoya baya, ya ƙare da kira na haɗa kai domin ƙara ƙarfafa matsayin APC a fadin Jihar Gombe kafin zaɓuɓɓukan gaba na 2027.

By ukarofi