Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Sabuwar Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ƙasa ta bayyana sunayen sabbin shugabannin ta na reshin Jihar Nasarawa tare da ƙaddamar da kwamitocin gudanarwar cewa sun haɗa da tsohon mataimakin gwamnan jihar ta Nasarawa, John Mike Abdul a matsayin shugaban kwamitin ɗin kuma kodineta haɗe da shugabam jam’iyyar a jihar duk shi kaɗai.
Sauran membobin kwamitin sun haɗa da:
Sen. Suleiman Adokwe- Mamba
Hon Adamu Oyanki – Mamba
Dr. Umar Musa Galadima – Mamba
Barr. John Matthew- Mamba
Hon. Musa Bako Karshi – Mamba
Prince Yamusa Chindo- Mamba
Sauran sune: Comr. Idris Ojoko Jibrin – Mamba
Hon. Aminu Nagogo – Mamba
Alhaji El-Mahmud Hussaini Sani – Mamba
Ms. Farida Umar- Mamba da dai sauran su da yawa.
An kuma bayyana sunayen wasu sanannen ‘yan siyasa daga ‘yankunan karkarar jihar ta Nasarawa a matsayin sabbin mambobin wani kwamitocin da zai riƙa kula da gundumoin ƙananan hukumomin jihar 13.
A jawabin sabon Shugaban kwamitin din wanda a yanzu yana kuma matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar ADC ɗin a jihar John Mike Abdul jim kaɗan bayan an ƙaddamar da shi da sauran shugabannin a duka matakai ya godewa uwar jami’iyyar ta ƙasa dangane da zaɓin sa a muƙamin inda ya kuma umurci sabbin membobin kwamitocin da su kasance masu adalci da kuma numa gaskiya da riƙon amana wajen aiwatar da ayukan su.
Ya kuma ƙalubalance su su tabbatar sun yi aiki tuƙuru a yankunan su musamman yankunan karkara don tabbatar sun samu nasara a duka zaɓukan kujerun siyasa na 2027 dake tafe kana ya buƙaci suyi aiki tare don cimma burin jam’iyyar ADC a jihar ta Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya.
Suma a nasu ɓangaren shugabannin kwamitin ƙananan hukumomin sabbin duk sun tabbatar cewa za su haɗa kai wajen shigar da sabbin membobi a jam’iyyar domin lashe dukan kujeru a zaɓen 2027.
Wakilin mu a jihar dai ya lura cewa wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun haɗa da:
Sen. Mohammed Ogoshi Onawo. Mataimakin shugaban ADC na ƙasa (Arewa) da kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu da
Sen. Patricia Akwashiki da shugaban ma’aikatan shugaban ADC ɗin na ƙasa Hon. Barr. Musa Elayo da mataimakin shugaban ADC na ƙasashen waje (Diaspora) da kuma tsohon Ministan Shari’a Barr. Mohammed Abdullahi da tsohon ministan Muhalli
Hon. Abdulkarim Ombamas da ɗan takarar PDP na 2023 wanda ɗan mazaɓar Nasarawa Eggon, da Akwanga da Wamba ne wato Gen. Nuhu Angbazo mai ritaya da sauran su da dama.
Taron ƙaddamar da sabbin shugabannin da mambobin sabuwar jam’iyyar ADC ɗin na jihar ta Nasarawa ta gudana ne a babban ɗakin taro na wani otel da ake kira Otunsha Hotel dake birnin Keffi da yammancin ranar Talata na mako da ake ciki kuma har ila yau wakilin namu ya gano cewar galibin sabbin shugabannin ADC ɗin a jihar tsofaffin jiga-jigan ‘yan babban jam’iyyar adawar nan ne a jihar wato PDP waɗanda ada suka riƙe manyan muƙaman siyasar a inuwar PDP ɗin a ciki da wajen jihar na tsawon lokaci.
