
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta sako tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal bayan cika sharuɗɗan beli.
Sannan ta gargaɗi jam’iyyar ADC bisa zargin EFCC’n da yunƙurin siyasantar da bincike akan lamarin da ya shafi rashawa.
A ranar Litinin jami’an EFCC suka tsare Tambuwal a hedikwatarsu bayan ya masa gayyatar da suka yi masa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan ya je ofishin hukumar ne da misalin ƙarfe 11:16 na safe, sakamakon zargin sa da hannu a badaƙalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai kimanin Naira biliyan 189 daga asusun gwamnatin jiharsa a lokacin da ya ke gwamna.
Wani jami’in hukumar da ya nemi sa ɓoye sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa an tsare Tambuwal ne bayan ya ƙi bada gamsassun amsoshi game da tambayoyin da aka yi masa yayin binciken.
Akan haka ne kuma EFCC ta yi martani ga ADC bayan jam’iyyar ta zarge ta da harin ƴan siyasar da ke ɓangaren adawa, lamarin da Shugaban EFCC Ola Olukoyede ya yi watsi da shi inda ya ce an yi haka ne don a ruɗar da al’umma.
“Babu iyaka akan binciken manyan laifuka. Damfara damfara ce. Rashawa rashawa ce”, inji Olukoyede.
Ya kuma ce, babu maganar jam’iyya ko ɗaukar wani ɓangare a aikinsu, inda bincikensu zai iya hawa kan kowa ciki har da gwamnoni masu ci, ministoci da jiga-jigan jam’iyya mai mulki.
