Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
A lokacin bikin ranar matasa ta duniya da aka gudanar a Gombe, shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar (ALGON), Barista Sani Ahmad Haruna, ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin Gombe State Traffic and Environmental Corps (GOSTEC) a matsayin cikakkun ma’aikata.
Ya ce matakin ya nuna jajircewar gwamnati wajen tallafawa matasa domin rage zaman banza da inganta rayuwarsu.
“Yanzu wasu daga cikinsu sun zama masu amfani ga kansu da al’umma, saɓanin yadda rayuwarsu ta kasance a baya,” in ji shi.
Barista Sani ya yi kira ga matasa da su kasance masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, yana mai jaddada cewa su ne ginshiƙan cigaban kowace al’umma.
Ɗaya daga cikin matasan da aka ɗauka, Musa Abdullahi, ya bayyana cewa shirin GOSTEC ya sauya masa rayuwa daga neman aiki zuwa bayar da gudummawa ga tattalin arzikin jihar.
Haka zalika, Fatima Mohammed, ta nuna farin cikinta da samun aikin gwamnati bayan samun horo a fannin tsara shafukan intanet, tana yabawa ƙoƙarin gwamnati na inganta makomar matasa.
Bikin ya samu halartar jami’an gwamnati, ƙungiyoyin matasa da na farar hula, tare da tattaunawa kan makomar matasa, ilimi da bunƙasar tattalin arziki a jihar.
