Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kai wani ziyarar gani da ido na musamman zuwa gidan yarin nan dake Keffi a jihar inda wasu fursunoni 16 suka tsere a makon nan.
Idan ba a manta ba a ranar Talatar mako da ake ciki ne jaridar Manhaja mai farin-jini ta ruwaito labarin tserewa da wasu daga cikin fursunonin gidan yarin dake birnin Keffi a Jihar ta Nasarawa su 16 suka yi inda daga bisani hukumar gidan yarin ta sanar da kamo mutum huɗu daga cikin su.
A halin da ake ciki dai a yanzu haka gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule a yayin ziyarar na musamman da ya kai gidan yarin wato wayewar garin aukuwar lamarin jiya Laraba 13 ga watan Agustan shekarar nan 2025 kenan ya bayyana takaicin sa dangane da yadda a cewar sa ake tara masu laifi da yawa a gidajen fursunonin jihar da ƙasa baki ɗaya kamar ba mutane ba tare da an kuma saurari shari’ar su ba da hakan nema a cewar sa ke jawo ire-iren mumuman lamarin.
Wakilin gwamnan ya rubuto cewar a yayin ziyarar na musamman tare da rakiyar wasu manyan muƙarraban gwamnatin sa, jami’an gidan yarin sun zaga da shi sassan gidan yarin da gine-ginen musamman inda waɗanda suka tseren suka aikata ɗanyen aikin.
Da yake tattauna da manema labarai jim kaɗan bayan ya duba kayayyaki a gidan yarin gwamna Sule ya bayyana cewa tabbas fursunonin sunyi yawa fiye da kima a gidan yarin kuma galibin su waɗanda suke zaman jiran shari’ar sune a kotuna daban daban musamman a wasu kotunan da dama dake birnin tarayya Abuja da sauran su da daɗewa kuma ba ayi hakan ba har yanzu.
Gwamnan jihar ta Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kuma yi alƙawari cewa a nata ɓangaren gwamnatin sa za ta cigaba da nemo hanyoyi da suka dace wajen ganin an daina ɓata lokaci wajen sauraran ƙararraki a kotuna tare da yanke hukunci a lokuta da suka dace ba tare da ana cigaba da ɓata lokaci ba gaira ba dalili ba a fannin don rage cunkuso a gidagen yarin jihar gaba ɗaya kana ya shawarci fannin shari’ar ƙasar nan suyi la’akari da hakan.
Duk da hakan ya kuma yi amfani da damar inda ya buƙaci fursunoni da suka rage a gidan yarin da sauran gidajen yarin jihar da ƙasa baki ɗaya su kasance masu kyawawan ɗabi’u, su kuma riƙa kiyaye dokokin matsugunin su a ko yaushe.
Daga ƙarshe a wani yanayi na ban tautsayi, gwamnan bayan ya kuma lura cewa yawancin fursunonin gidan yarin na Keffi inda ya kai ziyarar suna zama ne a ƙasa kan siminti sai nan take ya umurci wasu daga cikin muƙarraban nasa su turo sabbin katifu (mattress) a kai gidan yarin ba tare da ɓata lokaci ba don inganta rayuwar fursunonin a gidan yarin.
