Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Da alamu tawadar alƙalami na kan Isra’ila bai ba ta bushe ba don yadda kusan kullum sai an samu wani muhimmin labara da kan ɗau hankalin duniya inda ya kan fidda halin ko in kula na wasu manyan ƙasashe da kuma damuwa daga wasu masu kadaran-kadahan. Yadda a ke zubar da jini a Gaza tamkar ba ma mutane ne ke zaune a wajen ba wasu itatuwa ne. Gaskiya akwai tabbacin an kafa ƙasar Isra’ila ne don wata manufa ta mamaye yankunan Larabawa da zama kandagarki ga duk mai son dagawa ƙasashen yamma masu nukiliya yatsa. Ba ma bambanci tsakanin ƙasashen yamma na wannan zamani da Isra’ila. Kai ni ina ganin Isra’ila ma wata jiha ce a yammacin duniya da ke da babban birni a yankin Falasɗinawa. Yanda hankalin ƙasashen da na ke magana ya kan tashi kan duk wani yunƙuri na kin amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu ko nuna takaici ga mamaye ƙasar Falasɗinawa na nuna a zahiri su ma jagororin wasu daga ƙasashen na yamma ainihin su Yahudawa ne don haka su na kare ’yan uwan su ne ko ta halin kaka. A zahiri akwai bambancin addini tsakanin Yahudawa da Nasara amma a siyasar duniya su kan iya zama sammakal. Shin akwai ma mai bin addinin nasara da ke ƙalubalantar addinin Yahudawa ne? in akwai me ya sa ba sa kai ɗauki ga ‘yan uwan su masu bin addinin nasara a tsakanin Falasɗinawa? Ina lura da cewa a na ɗaukar Falasɗinawa ma ba su da hurumin bin addinin Kirista. Haƙiƙa zan iya tsame sabon Fafaroma Leo wanda ya buƙaci kare sassan addini a hare-haren Isra’ila. Fafaroma ya yi magana ne lokacin da Firaministan Isra’ila ya buga ma sa waya biyo bayan ruwan wuta da sojan Isra’ila su ka yi kan majami’ar mabiya katolika ita ɗaya da ke Zirin Gaza ta kashe Falasɗinawa Kirista mabiya ɗarikar katolika. Ina sauran mabiya addinin Kirista na sauran ƙasashen duniya. Da alamun akwai Kiristocin da su ke matuƙar ƙaunar Isra’ila fiye da kowa ma a duniya kuma duk abun da Isra’ila ta yi daidai ne a wajen su wataƙila ko za ta kashe su ma za su iya ɗauka hakan ne mafi a’ala a gare su!. Mu bar ma batun addini mu koma kan yadda a ke kashe yara ƙanana da mata a Gaza. Sojan Isra’ila bas a tantance waye ma za su kasha tun da in dai mutum Bafalasɗine ne to shikenan ya jira lokacin kisa don an yanke ma sa hukunci saura zartarwa. Kun ga lokacin da Rasha ta ɗau haramar kwance damarar yaƙin ƙasar Yukrain sai duk manyan ƙasashen duniya su ka ɗau matakan mara baya ga Yukrain ɗin har da tura maƙudan kuɗi da makamai wasu ma har da takunkumin karya tattalin arzikin Rasha. Inda Rasha laga-laga ce ma da tuni sun kai ma ta farmaki na kai tsaye. Rashin sa’ar nasarar bijirewa da shugaban sojojin haya na Wagner Yevgeny Progozhin ya yi ya ɗan taka birki ga burin wargaza Rasha ma gaba ɗaya. Manyan ƙasashe ba sa marmarin yaƙi kai tsaye sai dai a kaikaice ko amfani da wata kasa wajen gwada ƙarfin su kamar yanda ya auku lokacin da Bashar Al’Asad ya ke shugabancin ƙasar Siriya. Mun ga yadda a ka marawa ‘yan tarzoma su ka wargaza Afghanistan har tsawon shekaru kimanin 20 kafin lura da ƙasar ba sauran ribar yin hakan a ka kyale ‘yan Taliban su ka dawo. Mu daina ganin laifin kauda-bara na wasu ƙasashen Larabawa kan kaucewa fito na fito da yammacin duniya. Matukar kasa na bin tsarin mulkin mulukiyya irin na zamanin da ya shude to dole sai shugabannin ta sun yi takatsantsan don gudun cinno mu su wutar da za ta laƙume su. Idan jama’ar ƙasa na zaune lafiya ba tsananin yunwa ba tashin boma-bomai to gara su mika wuya ga tsarin da su ke ciki don in sun nemi yin bore akwai waɗanda za su taimaka mu su amma ba da niyyar gaskiya ba sai don maida ƙasashen su sansanin yaƙi. Me ya sa har yau Sudan ta kasa dawowa daidai duk da ba Omar Elbashir ɗin da yammacin duniya su ka tsana ne ke kan gado ba?. Iraƙi da Libya duk sun zama sauran magagin yaki don zai yi wuya gari ya zube a iya kwashew duk.
Hukumomin Isra’ila sun haramtawa babban mufi na birnin Kudus da yankunan Falasɗinawa Sheikh Muhammad Hussein shiga masallacin AƙSA baitul muƙaddas na tsawon wata 6.
Matakin ya biyo bayan wata huɗubar da ya gabatar da ta nuna takaici ga matakan cusa yunwa ga al’ummar Gaza.
Gabanin wannan matakin, a ƙarshen watan jiya hukumomin na Isra’ila sun gayyaci Sheikh Hussein bayan wata huɗubar su ka haramta ma sa shiga masallacin na tsawon kwana 8 da kuma yiwuwar tsawaita haramcin.
Gwamnatin Falasɗinawa a birnin Ramallah ƙarƙashin shugaba Mahmud Abbas ta yi Allah wadai da wannan matakin.
Ma’aikatar harkokin addini ta Falasɗinawa ta ce hakan shiri ne na Isra’ila na cigaba da mamaye birnin ƙudus, Zirin Gaza da ma yankunan yammacin kogin Jodan da kakkaɓe hannun ma’abota addini daga masallacin na Al’aƙsa.
Wannan na zuwa daidai lokacin da sojojin Isra’ila kan buɗe wuta kan sashen masu taruwa don karɓar kayan agaji a Gaza da kan jawo asarar rayuka.
Sashen sojan Hamas wato Ezzeddine Al-ƙassam ya saki faifan bidiyo mai tsawon minti ɗaya da ke nuna ɗaya daga kamammun Isra’ilawa da ke cikin matuƙar yunwa a Gaza.
Al-ƙassam ta nuno kamemmen ne da Isra’ila ta gano sunan sa Evyatar David a wata hanyar ƙarƙashin aasa mai matsi ya na yanayin yankwanewa kamar yadda akasarin yaran Gaza su ke ciki don ƙarancin abinci sanadiyyar datse hanyoyin agaji da Isra’ila ta yi.
Evyatar David mai shekaru 24 da abokin sa Gal Gilboa na daga cikin mahalarta bikin raye-raye da wake-wake na NOVA da a ka gudanar a kudancin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba 2023, yayin da Hamas ta kawo farmaki ta yi awun gaba da su.
Cikin mutum 251 da Hamas ta ɗauka a NOVA, 49 na nan a Gaza ciki kuma da mutum 27 da sojan Isra’ila su ka ce sun mutu.
Jakadan shugaba Trump a fitinar Falasɗinawa da Isra’ila Steve Witkoff ya shiga garin Rafah don duba sassan da a ke raba kayan agaji ga al’ummar Gaza da ke cikin matsanancin yunwa.
Witkoff ya shiga garin na kuryar Gaza ta kudanci tare da jakadan Amurka a Isra’ila Mike Huckabee.
Duk sassa 4 da a ke raba kayan agajin ga waɗanda ke cikin matsananciyar yunwa na ƙarƙashin kulawar sojan Isra’ila ne.
Rundunar sojan Isra’ila da ke cewa ta kan yi harbin gargaɗi ne don tarwatsa cunkoso ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan masu dafifin karɓar agajin.
Ziyarar tamkar na nuna gwamnatin Trump na son maida hankali wajen kayan agaji su isa ga jama’ar Gaza da ware Hamas don yadda jami’an Amurka su ka fice daga taron sulhu a Katar da aza alhaki kan Hamas.
Hakanan Jakadan ya gana da ‘yan uwan kamammun Isra’ila da su ka rage a hannun Hamas tsawon wata 22 da a ke gudanar da yaƙi.
Steve Witkoff ya gana da ‘yan uwan kamammun a Tel’aviv na Isra’ila inda masu zanga-zanga su ka taru su na sowa ga jakadan.
‘Yan uwan kamammun sun buƙaci taimakon Witkoff don samun ‘yanto ‘yan uwan su da su ke fargabar dawowar su a raye.
Bayan taron cikin ɗaki, ‘yan uwan kamammun sun fitar da sanarwar cewa witkoff ya ba su tabbacin shugaban Amurka Donald Trump zai yi duk mai yiwuwa wajen sako ‘yan uwan na su.
Isra’ila dai na nuna matukar Hamas ba ta sako kamammun ba cikin sulhu to yaƙi zai cigaba.
Ba alamu Hamas za ta saurari barazana ko karfin sojan Isra’ila ga sako kamammun ba tare da cimma sharuddan sulhun ba.
Kimanin Falasɗinawa 40 sun rasa ran su a Gaza ciki da 10 da ke kokarin karɓar kayan agaji a cibiyar da Amurka ke jagoranta wajen raba kayan tallafi.
Wasu mutum 5 ma sun mutu don tsananin yunwa a yayin da ƙarancin abinci ke adabbar mazauna Zirin.
Kazalika sojan Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa kimanin 13 da su ka taru a mashigar Zikim ta shiga arewacin Gaza inda a ke raba kayan agaji.
Mutane kan yi nasarar karbar buhun fulawa bayan gwagwarmayar ko kuma su dawo a kan makara don rasa rai.
Falasɗinawa kan taru don zaman makoki a asibitin Al-Shifa inda a kan kawo waɗanda su ka samu raunuka da gawawwaki.
Majalisar ɗinkin Duniya ta ce fiye da Falasɗinawa 1000 su ka rasa rai a yunƙurin karɓar kayan abinci na agaji.
KAMMALAWA
ƙungiyar Hamas da ke mulkin Gaza ta ce faufau ba za ta ajiye makamai ba sai an tabbatar da kafa ƙasar Falasɗinu mai babbar birni a gabashin Birnin ƙudus.
Wannan martini ne mai zafi ga sharaɗin Isra’ila na dakatar da yakin Gaza don buƙatar lallai Hamas ta kwance damara; na kan gaba a buƙatun Isra’ila don samun tsagaita wuta na kwana 60 da ma dakatar da yaƙi kan Gaza.
ƙasar Masar da Katar da ke jagorantar tattaunawar sulhu a birnin Doha sun amince da tsarin Saudiyya da Faransa na kafa ƙasar Falasɗinu gefe da Isra’ila a matsayin hanyar maslaha.
Kazalika Masar da Katar sun amince da buƙatar Hamas ta miƙa makaman ta ga gwamnatin Falasɗinawa da kasashen yamma su ka amince da ita.
Tattaunawar bayan gida da Isra’ila don samun sulhu da Hamas na tsagaita wuta tsawon kwana 60 ta kasa cimma nasara.
