
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗalibin aji biyu da ke karatu a tsangayar koyon aikin likitanci a Jami’ar Obafemi Awolo ya halaka kansa, kamar yadda Kakakin jami’ar, Abiodun Olanrewaju ya bayyana a ranar Alhamis.
Ɗalibin mai suna Ajibola Ibitayo, ya ɗauki matakin ne bayan duba sakamakon jarrabawarsa a ranar Laraba, inda ya gano cewa sai ya sake maimaita sashi na biyu a wani zangon karatu bayan ya maimaita a zangon da ya gabata.
A sanarwar da kakakin ya fitar, an yi zargin ɗalibin, wanda mahaifinsa babban likita ne, da yi wa kansa allura a gidan iyayensa da ke Ejigbo a Jihar Osun.
Mataimakin Shugaban Jami’ar (VC), Farfesa Adebayo Simeon Bamire ya bayyana hakan a matsayin abin tausayi da ya jefa makusantansa da jami’ar cikin jimami.
Ya kuma kirayi iyaye da wakilai da su riƙa horar da ƴaƴansu akan fahimtar rashin nasara a matsayin wani ɓangare ne na gwagwarmayar samun nasara a rayuwa.
Haka kuma ya yi kira ga ɗalibai da matasa da su riƙa ganin rashin nasara a matsayin dama ta sauya akalarsu wajen yunƙurin cimma nasarori a dukkan ababen alherin da suka saka a gaba.
Har’ilayau, Farfesa Bamire ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalai da ƴan uwa abokan arziƙi da tsangayar ɗalibin da ma jami’ar baki ɗaya haƙurin juriyan rashinsa.
