
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya karɓi baƙoncin Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Sun gana ne a birnin tarayyar Nijeriyar akan batutuwan da suka shafi kasuwanci musamman a yadda suka shafi Nijeriya da ma a mataki na ƙasashen duniya.
A wata hira da manema labarai bayan kammala zaman, Okonjo-Iweala, wadda ta samu rakiyar Ministar Kasuwanci, Jumoke Oduwole, ta ce sun ziyarci shugaban ƙasar ne don ba shi ba’asi akan wani abin farin ciki, wanda aka samu nasarar cimmawa da taimakon matar shugaban ƙasa.
Ta ce, sun ƙaddamar da tsarin bada tallafin kuɗaɗe na harkar tattalin dijital daga WTO da Cibiyar Kasuwanci ta Ƙasa-da-Ƙasa da kuma tallafa wa mata don sun amfana da shi gami da samar wa kansu ayyuka.
Ta bayyana cewa, hakan wani ɓangare ne na samar da hanyoyin tallafa wa matan Nijeriya domin su bada tasu gudunmuwar ga harkokin tattalin ƙasar da kuma gina kansu.
Shugaba Tinubu ya gana da Okonjo-Iweala ne makonni biyu kafin ƙarewar wa’adinta na farko a muƙamin shugabancin WTO a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Okonjo-Iweala, wadda ƙwararriya ce kan harkar tattali da kuɗaɗe a mataki na duniya, ta kafa tarihi na zama ƴar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta jagoranci ƙasashe 164 da ke cikin WTO.
