*Ta ƙaryata malamin da ya ce an yi sulhu
*Har yanzu muna neman Turji ruwa a jallo, cewar jami’an tsaro
*Yadda ƙananan hukumomin Katsina ke yin sulhu da ‘yan bindiga
*Yadda yaran Turji suka sake sake aikata ta’addanci a Sakkwato
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD da BELLO A. BABAJI a Abuja da ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hedikwatar Tsaron Nijeirya ta musanta rahotannin da ke cewa ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya miƙa wuya a ƙarƙashin wata yarjejeniyar zaman lafiya da wasu malaman addinin Musulunci suka yi da shi a Jihar Zamfara, lamarin da ke nunu da cewa, ba lallai nde rahotannin su zamto gaskiya ba.
Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji.
Ya ce: “Turji bai miƙa wuya ba. Har yanzu muna neman sa.”
Turji na daga cikin manyan ’yan bindigar da ake nema ruwa-a-jallo a Nijeriya. Turji ya jagoranci kai wa al’umma hare-hare a Jihohin Zamfara da Sakkwato, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.
A kwanakin baya, an samu rahotanni cewa Turji, ya ajiye makamai kuma ya saki mutum 32 da ya sace, bayan zaman sulhu da malaman addinin Musulunci suka jagoranta a Jihar Zamfara. Amma sojojin sun bayyana cewa wannan rahotanni ba gaskiya ba ne.
Hedikwatar Tsaron ta yi watsi da waɗannan iƙirari, tana mai cewa ba su da tabbaci kuma ba sa wakiltar wata tattaunawa ta gwamnati a hukumance.
Kangye ya kuma mayar da martani kan rahotannin baya-bayan nan da ƙungiyar Amnesty International ta yi na zargin sojojin Nijeriya da kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas, inda ya ce zargin ba shi da tushe.
“Sojoji ba su aikata wani kisan gilla ba a Kudu maso Gabas. Dole ne mutane su fahimci cewa ba kowane bidiyo ko da’awar yanar gizo ke bayyana gaskiya ba,” inji shi.
Dangane da zanga-zangar da wasu sojoji da suka yi ritaya suka yi a baya-bayan nan, Kangye ya bayyana cewa wasu mutane ƙalilan ne suka halarci taron, kuma hukumar kula da fansho ta soji, da hedikwatar tsaro, da kuma ministan kuɗi sun gana da tsoffin sojojin da suka ji rauni domin magance matsalolinsu.
Janar Tukur Gusau, ya ƙara da cewa, a kwanan baya Babban Hafsan Tsaron ƙasar ya gana da kwamitin mutum biyar da ma’aikatar tsaron ƙasar ta kafa domin gudanar da ayyukan inganta jin daɗin tsoffin sojoji.
Yadda ƙananan hukumomin Katsina ke yin sulhu da ‘yan bindiga
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
ƙaramar Hukumar Safana a jihar Katsina ta shiga jerin ƙananan hukumomin da suka amince su yi sulhu da ‘yan bindiga, domin kawo ƙarshen tashin hankali a yankin.
Wannan mataki ya biyo bayan irin yarjejeniyar da hukumomin Jibiya da Batsari da ɗan Musa suka ƙulla a baya, wacce ta kawo raguwar hare-hare da tsaro ga mazauna yankunan.
Yarjejeniyar ta ba da damar manoma su koma gonakinsu cikin kwanciyar hankali, ‘yan kasuwa su yi kai kayayyakinsu zuwa kasuwanni, da kuma bai wa ‘yan bindiga damar zuwa asibitoci da kasuwanni da yin zirga-zirga ba tare da tsangwama ba.
Shugaban ƙaramar Hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya bayyana cewa ba ‘yan bindigan da kansu ne suka nemi a yi sulhu.
Ya ce hakan ya faru ne saboda nasarar da aka gani a hukumomin da suka riga suka shiga wannan tsarin.
“Mun kafa ƙa’idoji a tsakanimu, inda muka amince cewa za su daina kai hare-hare a duk faɗin ƙaramar hukumar Safana, kuma su sako duk mutanen da ke hannunsu.
“‘Yan bindigar kuma sun nemi mu gyara musu madatsun ruwa da dam-dam domin shayar da dabbobinsu, tare da gyaran asibitoci da makarantu da islamiyyoyi domin koyar da ‘ya’yansu ilimin zamani da na addini,” inji shi.
Abdullahi ya ce sakamakon wannan mataki da ya ƙarfafa gwiwar ‘yan bindigan, sun buƙaci ƙananan hukumomin Kurfi da Dutsinma su shiga cikin yarjejeniyar, kuma ya ce yana da yaƙinin cewa nan ba da jimawa ba za su amince.
A cewar wani mazaunin garin Safana, Iliyasu Sani, al’umma na amfana sosai daga wannan sulhu.
“Yanzu muna fita kasuwa cikin natsuwa, muna noma ba tare da tsoro ba, harkokin yau da kullum suna tafiya yadda ya kamata. Idan na kwatanta da shekaru uku da suka gabata, yanzu zaman lafiya ya dawo,” inji shi.
Masani kan harkokin tsaro, Dr Kabiru Adamu, ya bayyana cewa matsin rayuwa da rashin tsaro ne suka tilasta wa al’umma neman mafita da kansu.
“Jama’a sun gaji da halin da ake ciki, kuma hukuma ba ta kare su yadda ya kamata. Duk da cewa gwamnatin Katsina ta sha nanata cewa ba za ta nemi sulhu da ‘yan bindiga ba, ta bayyana cewa idan ‘yan bindigan suka nemi sulhu tare da ajiye makamai, ba za ta hana ba,” inji shi.
Dr Kabiru ya ƙara da cewa, idan aka tabbatar da bin ƙa’idoji da tsayawa a kan alƙawura, wannan sulhu na iya zama matakin farko na wanzar da zaman lafiya na dindindin a yankin.
Masanin ya ƙara da cewa wannan sulhun da Safana ta shiga na iya zama wani sabon babi na farfaɗo da rayuwar al’umma a yankin, inda manoma, ‘yan kasuwa da talakawa za su koma harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Amma zaman lafiya zai tabbata ne kawai idan an tabbatar da cewa dukkan ɓangarorin sun tsaya tsayin daka kan abin da aka cimma, musamman wajen daina laifuka da tabbatar da tsaro ga kowa da kowa inji shi.
Yaran Turji sun sake sake aikata ta’addanci a Sakkwato
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ‘yan bindiga daga dabar shahararren jagoransu, Bello Turji, sun kai sabon hari a ƙauyen Garki da ke jihar Sakkwato, inda suka yi awon-gaba da mutane 16 da halaka ɗaya da kuma ɗebe dabbobi da dama duk da iƙirarin ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da wakilan gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa, harin, wanda ya auku a yammacin ranar Laraba, an yi shi ne ƙarƙashin jagorancin makusancin Turji mai suna Kallamu da ‘yan barandarsa.
Wani shaida ya ce, ‘yan bindigar sun isa yankin ne a adadi mai yawa inda suka ta yin harbe-harbe, kana daga bisani suka yi garkuwa da mutane da sace wasu dabbobi.
ƙwararre kan sharhin harkar tsaro, Zagazola Makama ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an ƙaddamar da harin ne a irin salon Turji, inda aka fara da yin harbe-harbe gabannin ɗaukar mutanen.
Al’amarin dai ya haifar da rashin tabbas game da matsayar Turji na kira da a yi sulhu musamman a baya-bayan nan da aka yaɗa na tsakaninsa da malaman addini da wakilan gwamnati.
Sanannen ɗan bindigar ya sha kira da a yi sulhu domin kawo ƙarshen ayyukansu na ta’addanci, saidai ana ganin hakan kamar akwai yaudara a ciki, saboda a duk sadda aka tattauna da shi, daga bisani sai ‘yan dabarsa sun kai hari ko garkuwa ko kashe mutane, kamar yadda wata majiya ta tsaro ta shaida.
Rahotannin sirri sun shaida wa manema labarai cewa har yanzu ayyukan ta’addancin Turji na cigaba da gudana a yankunan Isa, Sabon Birni da Goronyo tare da ‘yan bindiga da dama da ke kai kawo tsakanin Nijeriya da Nijar.
