Tattalin arzikin Nijeriya na samun ƙarin daraja a idon duniya – Minista

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kan ‘Yan ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun yabo daga hukumomin kimanta tattalin arziki na ƙasa da ƙasa, wanda ke nuna ƙaruwar amincewa da alƙiblar da ƙasar ta ɗauka.

Idris ya bayyana hakan ne bayan ganawar sa da Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, a Abuja.

Ya ce shirin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yana haifar da sakamako mai gamsarwa ga ƙasa.

A cewarsa, hukumomin kimanta tattalin arziki na duniya sun inganta ra’ayin su game da Nijeriya sakamakon ci gaba da ake samu a ɓangaren gyare-gyaren tattalin arziki da aiwatar da manufofi.

Ya jaddada cewa duk da har yanzu ba a cimma cikakken buri ba, shirin gwamnatin na tafiya bisa tsari, kuma ana kan hanyar kaiwa ga burin cimma tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya da Shugaba Tinubu ya yi alƙawari.

Idris ya ƙara da cewa, ana samun ci gaba a fannin wadatar abinci da yaƙi da rashin tsaro, yayin da tsarin rabon kuɗaɗen gwamnati ke bai wa gwamnati a matakan tarayya da jihohi ƙarin damar gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Ya bayyana cewa ganawarsa da Uzodimma wani ɓangare ne na tuntuɓar juna tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi don daidaita dabarun aiwatar da manufofin gwamnati.

Ministan ya jaddada muhimmancin sanar da ‘yan ƙasa ci gaban da gwamnati ke samu, yana mai cewa aikinsa shi ne tabbatar da cewa jama’a sun san irin ƙoƙarin da ake yi don inganta rayuwar su.

By ukarofi