Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ofishin yaɗa labarai na Dekta Kayode Fayemi, tsohon gwamnan Ekiti, ya yi watsi da wata iƙirari da ake yaɗawa daga Rotimi Amaechi na cewa mutanen biyu ne suka kafa sabuwar jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Ameachi tsohon Gwamnan Ribas ne kuma tsohon Ministan Sufuri a ƙarƙashin Marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ofishin yaɗa labarai na Fayemi, Malam Ahmad Sajoh, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Sajoh ya ce, babu wata kwakkwarar hujja, da suka haɗa da bidiyo ko rahotanni masu inganci da za su iya tabbatar da iƙirarin Amaechi.
Ya bayyana rahoton a matsayin “maiyuwa ƙage ne ko kuma kuskure,” yana gargaɗin jama’a game da labaran ƙarya da kafafen sada zumunta ke yaɗawa.
A gare shi, Fayemi ya kasance jajirtacce a jam’iyyar APC a jihar Ekiti kuma ya fito fili ya amince da Gwamna Biodun Oyebanji ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin tikitin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa, yayin da Fayemi ke ci gaba da tattaunawa a tsakanin jam’iyyu domin ci gaban ƙasa, hakan ba ya nufin ta fice daga jam’iyyar APC.
Ya alaƙanta raɗe-raɗin da ake yi game da Fayemi a siyasance da ƙarancin ganinsa a ƙasa saboda karatun da yake yi a Kwalejin King London da kuma aiki a Cibiyar Amandla, ya ƙara da cewa ya ci gaba da taka rawar gani a taron shugabannin APC a Ekiti.
“Duk da ƙoƙarin tabbatar da wannan bayani da ya samu karɓuwa a kafafen sadarwa na zamani, ba mu samu wata kwakkwarar hujja da ta tabbatar da hakan ba, kuma babu wani faifan bidiyo.
A cewarsa, Fayemi a tarukan al’umma daban-daban a Ekiti da sauran wurare ya sha nanata kwazonsa ga jam’iyyar APC, tare da ƙoƙarin magance ƙalubalen da take fuskanta da kuma ciyar da manufofinta na ci gaba ga Nijeriya.
“Bugu da ƙari, Dokta Fayemi ya fito fili ya amince Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, domin ya sake tsayawa takara, inda ya goyi bayan takarar sa na tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC.
“Wannan ya nuna biyayyarsa ga APC. Muna kira ga jama’a da su kula da duk wani labari da ya shafi Fayemi, musamman idan ya samo asali daga kafofin sada zumunta,” inji shi.
