Atiku ya jinkirta karɓar katin ADC ana tsaka da raɗe-raɗin takarar Jonathan a PDP

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta karɓar katin zama cikakken memba a jam’iyyar ADC a hukumance, lamarin da ya janyo cece-kuce kan rikicin siyasa da ya kunno kai da tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ake raɗe-raɗin zai iya koma wa takarar shugaban ƙasa na 2027 a Jam’iyya PDP.

Atiku wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar PDP bayan da aka daɗe ana taƙaddama, an shirya zai karɓu katin zama ɗan jam’iyyar ADC a mahaifarsa ta Jada, jihar Adamawa a ranar 6 ga watan Agusta.

Bikin, wanda aka shirya yi a ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, an ɗage shi sai baba ta gani ba tare da wani bayani a hukumance daga ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba.

Haka zalika, wani jigo a jam’iyyar ADC ya shaida wa jaridar PUNCH cewa jam’iyyar ta yi ta tattaunawa da Jonathan kan yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Da yake zantawa da jaridar, shugaban jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa, Shehu Yohana, ya ce an zage rajistar da Atiku zai yi a jam’iyyar ba tare da wata sabuwar rana ba.

A halin da ake ciki kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC a matakin ƙasa, wanda ba ya son a bayyana sunan sa, ya shaida cewa ɗage karɓar katin jam’iyyar ba zai rasa nasaba da rigimar iko ba tsakanin Atiku da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Jigon jam’iyyar ya yi zargin cewa tafiyar siyasa ta Obi ta kwace jam’iyyar ADC a Kudu, lamarin da ya ce ya jefa burin Atikun na zama shugaban ƙasa cikin barazana.

A cewar shugaban jam’iyyar ADC na Adamawa, Shehu Yohana, Atiku ya nuna cewa a yanzu haka bikin zai gudana ne a tsakiyar watan Agusta ko kuma daga baya, mai yuwuwa a watan Satumba, yayin da yake jiran ficewar wasu gwamnonin APC zuwa jam’iyyar ADC.

Wasu majiyoyi sun shaida cewa jinkirin na iya nasaba da rikicin madafun iko a cikin ADC, inda ake zargin abokan tsohon ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ne ke riƙe da reshen kudancin jam’iyyar – wanda ke dagula burin Atikun na shugaban ƙasa.

Wasu majiyoyi na nuni da cewa Atiku na iya komawa jam’iyyar SDP idan lamarin ya ta’azzara.

A halin da ake ciki kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC ya bayyana cewa, jam’iyyar na tattaunawa sosai da Jonathan, wanda rahotanni suka ce a shirye yake ya shiga, amma ba ƙarƙashin PDP ba, saboda tasirin Nyesom Wike a cikin jam’iyyar.

Tuni dai jita-jitar dawowar Jonathan ta fara janyo cece-kuce a yanar gizo, inda hotunan yaƙin neman zaɓe suka haɗa shi da abokan takararsa daban-daban ciki har da Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso.

Sai dai uwargidan Jonathan Patience ta fito fili ta bayyana cewa tana goyon bayan uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu kuma ba ta da shirin komawa fadar Aso Rock.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya yi watsi da duk wata shawara da ke nuna cewa yiwuwar yunƙurin Jonathan ne ya janyo tsaikon da aka samu, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da rajistar, kuma Atiku ba ya barazana ga kowane abokin hamayya.

Ya zargi APC da yunƙurin tada zaune tsaye a ADC don cire Atiku daga zaɓen 2027.

Jami’an ADC na kasa sun kuma zargi jam’iyya mai mulki da ɗaukar nauyin tashe tashen hankula a cikin gida a wani yunƙuri na raunana jam’iyyar gabanin zabe.

Rikicin cikin gida a cikin ADC na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta tsayar da kanta a wasu muhimman fafatawa da ke tafe, ciki har da takarar gwamnan jihar Osun a 2026.

By ukarofi