Daga RABI’U SANUSI a Kano
Yanzu haka shiri yayi nisa dangane da zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a wasu ƙananan mazaɓu na ƙaramar hukumar Ɓagwai na ɗan majalisar jiha da ke Jihar Kano.
Ɗaya daga cikin mazaɓun sun haɗa da mazabar Kiyawa dake ƙaramar hukumar Ɓagwai, inda a cikin hotunan nan ke nuna al’umma sun hau layi za a fara tantance su dan su fara jefa ƙuri’a.
Haka kuma suma a garin ƴan kifi da ke mazaɓar Ƴan Dadi a yankin ƙaramar hukumar Ghari da a ka fi sani da (KUNCHI) suma sun hau layi dan fara gudanar da zaɓen wanda suke da ra’ayi.

