
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Lauyan ƙare ƴancin al’umma Ayodele Ademiluyi ya shigar da Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama (NCAA) da wasu ɓangarori ƙara bisa saɓa wa doka wajen cin zarafi da ya haɗa mawaƙi King Wasiu Ayinde Marshal da wata fasinja mai suna Comfort Emmanson.
Sauran waɗanda ya zayyano a takardar ƙarar sun haɗa da hukumomin FAAN, NCoS, AON da NPF, sai kuma gwamnan jihar Akwa-Ibom da Antoni Janar na jihar.
Lauyan ya zarge su da karya dokar ƙasa wajen yin hukunci game da lamarin mutane biyun, wato King Wasiu Ayinde Marshal da Comfort Emmanson.
Ya kuma zargi Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo da ɗaukar ɓangare a madadin ya yi ƙoƙarin tabbatar da doka yayin tsoma baki a lamarin.
Don haka ya roƙi kotu da ta yi hukunci akan duk wanda ta samu da laifi a ciki ba tare da la’akari da muƙaminsa ba kasancewar doka tana gaba da kowa.
