An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya sabunta cinikayya da ƙungiyar dillalan jaridu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Anyi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya dawo da shirin nan na sayen jaridu a wajen ya’yan ƙungiyar a Katsina.

Gwamnatin Katsina ta daɗe tana sayen duk wata jarida da aka kawo Katsina,inda ake aikawa ofishin gwamna da mataimakin sa da sauran wasu mahimman ma’aikatun gwamnati.

A wajen wasu mambobi na ƙungiyar gwamnati ke saye inda a karen wata a biya.

To sai dai daga baya gwamnati ta tsaida saye wanda hakan a cewar Muhammad Rabi’u wanda ke sayar da jaridu a Sabon Layi Katsina ya jefa mafi yawan ya’yan ƙungiyar cikin halin ƙuncin rayuwa.

“Ya ce wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya sa mafi yawan masu wannan sana’a cikin ƙuncin rayuwa,wasu kuma sun bar sana’ar,”inji Malam Rabi’u.

Rabi’u wanda babban dillali ne da yake rabawa ya’yan ƙungiyar jaridu a faɗin jihar ya bayyana cewa wasun su sun koma sayar da ruwa a kan manyan hanyoyi,wasu koma ƴan Okada.

Sai yayi kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya taimaka ya dowo da tsarin ko don ya’yan ƙungiyar sa farfaɗo daga ƙuncin rayuwa da suka tsunduma ciki.

Rabi’u na nuna damuwarsa kan yadda a kwanan baya ana kawo masa jaridu daban daban har gida, sai dai daga gidajen jaridu na ƙasan, amma yanzu gidajen jaridu biyar ne kawai ke kawowa.

Haka shima tsohon shugaban ƙungiyar jami’an yaɗa labarai na ƙananan hukumomi a jihar Abdu Bawa Dutsinma mahimmancin farfaɗo da sayen jaridu da gwamnatin Katsina ta saba saye.

Ɓullar kafofin sadarwa shima ya taimaka wajen gurgunta sana’ar sai dai ba ma a Katsina ba har ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi