Ministan Labarai ya yi godiya ga Tinubu kan umarnin sake gina gadar Mokwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma Mohammed Idris ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa amince wa sake gina gadar Mokwa a Jihar Neja.

Da yake magana yayin ziyartar Ministan Ayyuka, Dave Umahi a Abakaliki, Babban Birnin Jihar Ibonyi, Ministan Labaran ya ce, suna godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa gami da farin ciki da hoɓɓasan.

Gadar ta lalace ne sakamakon wani gagarumin ruwan sama da aka yi a watan Mayu, 2025, lamarin da ya yi sanadin ambaliyar da ta ɗaiɗaita dubunnan mutane da dama da lalata gidaje.

Haka kuma an rasa rayukan sama da mutane 200 a sanadiyyar iftila’in.

Ana sa ran gadar wadda mahaɗa ce tsakanin Arewaci da kudancin Nijeriya, sake gina ta zai lanƙwame kimamin Naira biliyan 16.7.

A nasa jawabin, Dave Umahi, ya ce Shugaba Tinubu ya amince da aikin ne bayan da Ministan Labaran ya gabatar masa da buƙatar hakan.

By Babaji