Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rahotanni daga waɗansu sassan Jihar Kebbi da suka haɗa da kananan hukumomin Danko, Wasagu Sakaba da Fakai da kuma Zuru daga ɓangaren Masarautar Zuru da kuma ƙaramar Hukumar Shanga daga Masarautar Yauri da ƙananan hukumomin Koko da Maiyama da Suru da Bunza daga Masarautar Gwandu sai ƙananan hukumomin Augie da Arewa na nuni da cewa, sun fi shan wahalar rashin tsaro, inda yanzu haka tafiye-tafiye da zuwa gona a waɗannan sassan ya zama wani abin tashin hankali da zulumi sanadiyyar rashin tabbas ga rayuwa ko a dawo ko kuma a haɗu da ajali.
A hanyar da ta tashi daga garin Argungu zuwa Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar bai fi kilomita 70 ba, amma shingen jami’an tsaro daban-daban ya kai kusan 50 a inda aka fito, amma yanzu ba su wuce biyar zuwa 10 ba, su ma sai dai a ranar kasuwa kurum, inda ke zargin za ka gan su a hanya suna tatsar kuɗi a hannun direbobi sanadiyyar waɗannan ’yan bindiga yanzu har a can su ke kai wa jami’an tsaron farmaki.
Wani mazaunin garin Bagiza da ke kusa da iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a yankin ƙaramar Hukumar Arewa da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa, su yanzu har sun saba da Lakurawa, saboda suna zuwa cikin garuruwansu kowane lokaci suna sayayya kuma suna gaya musu cewa, ba za su taɓa su ba sai dai da wani dalili. Ya kuma bayyana cewa, Lakurawan suna da aƙidar ƙyamar saka ƙananan tufafi da aka fi sani da ‘English Wears’ da kuma aske gashin gemu da kuma shan sigari da dai sauran ɗabi’un da su ke ganin shari’ar Musulunci ba ta yarda da su ba.
Satin da ya gabata waɗansu mutane akan babura da ake sa ran Lakurawa ne sun yi ɗauki ba daɗi tsakaninsu da wani ayari na gamayyar jami’in tsaro a mahaɗar hanyar da ta haɗa garuruwan Birnin Kebbi, Babban Birnin jihar, da Kangiwa da kuma Bui, inda jami’an tsaron suka sami nasarar kashe mutum ɗaya daga cikin Lakurawan, sannan waɗansu suka gudu da raunuka.
Haka zalika satin da ya gabata waɗansu da ake sa ran Lakurawa ne sun sun shiga yankin Arewa ta Gabas, inda suka bi garuruwa tun daga Dogon Daji, Gyarakamshi da Sakkwabe suka kwashe dukiyar mutanen garin tare da jikkata waɗansu.
Wani daga cikin shugabannin matasan yankin ya bayyana cewa, “ba za mu cigaba da haƙurin haka ba, wai a ce sai an zo an kashe mutane, sannan gwamna ya zo ya kawo kuɗi tambaɗe wai a ce a raba wa iyalan mamata da waɗanda suka jikkata, sannan kuma a ce wai idan waɗannan ɓarayin suka kawo hari kada a motsa. Maganar gaskiya wannan ba za ta saɓu ba.”
Ya yi kira ga matasan Arewa, inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata su haɗa kai su ƙalubalanci waɗanda ya kamata cikin lumana, don kawo ƙarshen ta’adanci a ƙaramar Hukumar Arewa, musamman ta hanyar zaƙulo masu tsegunta wa waɗannan ɓarayin sirrin mutanen gari da aka fi sani da ‘Informer’, saboda su ne babbar masifa ta farko da ya kamata a soma yaƙi da ita.
Ya ƙara da cewa, yanzu haka duk uwayen ƙasa da ke ƙaramar Hukumar Arewa sun kwashe iyalansu sun koma Argungu, waɗansu kuma sun koma Birnin Kebbi. Sai dai su kan shigo a tsorace, idan buƙatar hakan ta taso.
Rahotannin sun nuna cewa, shi ma Shugaban ƙaramar Hukumar Arewa, Hon. Sani Aliyu (Kulita), ya koma zuwa garin Birnin Kebbi tarre da iyalansa bakiɗaya.
Haka zalika bayanai sun nuna cewa, su ma jami’an tsaro da ke da kusan shingen bincike a kan hanyar da ta taso daga Argungu zuwa garin Bachaka kusan guda 50 yanzu sun watse, sai dai ranakun waɗansu kasuwanni kaɗai za ka gan su a hanya a tsorace suna tatsar kuɗi hannun direbobi.
A yankin ƙaramar Hukumar Augie, musamman daga garin Mera zuwa Dunaye zuwa Kalgo da ke kan iyakar jihohin Kebbi da Sokoto, ya zama wani tarko, inda ɓarayin dajin suka ɗauki salon tare hanya suna kore shanu ko kuma sukan kai samame a godajen da ke akwai shanu su kama, wani lokacin har sukan kashe masu shanun.
Bayanai a baya-bayan nan sun nuna cewa, dai yanzu haka dai waɗannan mayaƙan Lakurawa sun yi yawa a dajin Gulma da ke ƙaramar Hukumar Argungu da wani sashe na ƙaramar Hukumar Augie, yayin da su ke riƙe da iko a ƙaramar Hukumar Arewa, wanda har ta kai ga sun saka dokar hana saran itace, saboda su sami mafaka.
Wani matashi daga ƙauyen Saminaka da ke ƙaramar Hukumar Shanga ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, su masu garkuwa da mutane ne suka addabi yankin, saboda a cewarsa, yana da wahala a sati ba a ɗauki waɗansu mutane, don neman kuɗin fansa ba, kuma abin mamaki shine waɗannan mutanen ba nesa su ke da garuruwansu ba, inda su ke ajiye mutanen da suka ɗauka ba, sannan kuma ba sa tare hanya, sai dai su kan shigar gari ne cikin dare su shiga gida-gida ko kuma sukan yi wa wani ɗan kasuwa dirar mikiya a gidansa su yi gaba da shi.
Sai dai duk da irin batutuwan da Gwaman Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris, ke cewa, na gwamanti tana iya ƙoƙarinta kan harkar tsaro, ana hasashen jami’an tsaro suna sako-sako da lamarin saboda a duk lokacin da aka ce ga waɗansu ’yan bindiga sun kawo hari a wani gari, ba za su tafi ba har sai bayan an gama kwashe dukiyar mutanen garin an kuma kashe na kashewa, sannan su zo suna harbin iska.
A baya-bayan nan yayin wata ziyara da Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya kawo a Jihar Kebbi, Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana ƙudirinsa na yaƙi da waɗannan ’yan ta’adda, inda ya bayyana cewa, nan ba da daɗewa ba za a shirya wani sansani na sojojin sama a jihar.
Sai dai a ɓangaren hukumomin tsaro, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ta Kebbi, CP. Bello M. Sani, a koda yaushe ya kan yi kira ga al’ummar jihar da su riƙa sanar da hukumomin tsaro da ke kusa da su a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su yarda da shi ba.
