Akwai buƙatar iyaye su rinƙa ziyarar makarantun ‘ya’yansu – Shugaban makarantar sakandaren Daneji                  

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Malam Amin Abdullahi shi ne shugaban makarantar sakandare da ake kira Daneji Amintacciya da ke uguwar Daneji wadda tsohon A.G na ƙasa Ahmed Idris ya gina wa al’umma a ƙaramar hukumar birnin Kano da kewaye.

Shugaban Makarantar Malam Aminu ya ce akwai buƙatar iyayen ɗalibai a ko’ina su riƙa kai ziyara makarantun ‘ya’yansu don ganin yadda yaransu ke ɗaukar darasi wanda hakan zai ƙarfafawa malamai da ɗalibai gwiwa a makarantu, inda kuma ya shawarci iyaye kansu su bai wa hukumar makaranta da ƙungiyar iyaye da malaman makaranta haɗin kai ta hanyar biyan kuɗin PTA domin kowa ya bada gudunmawarsa wajen tallafin ilimi kamar yadda gwamnatin Kano da irinsu AG ke yi kodayaushe.

A ƙarshe Malam Aminu Abdullahi shugaban makarantar sakandare ta Daneji Amintacciya ya yaba wa Ahmad Idris kan gina wannan makaranta domin amfanin unguwannin Jakarta, Daneji Soron ɗinki, Makwarari, Mandawari, da dai sauran maƙotan unguwanni wanda Ubangiji kaɗai ya san wanda za su amfana da wannan makaranta ta Daneji wanda tsohon AG ke ƙoƙarin faɗaɗata don samun ɗakin kwamfuta da ɗakin karatu kamar dai yadda ya saba tallafawa a fannin ilimi, lafiya, koyar da sana’o’i da kuma yin amfani da damar wajen ɗaukar matasa aiki da ma buƙatar kowa ya yi koyi da shi wajen tallafawa da kyautatawa al’umma.

By ukarofi