Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugabar ƙungiyar Mar’atussaliha mai rajin kare mutuncin marayu da zawarawa da ke reshen ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Hajiya Mariya Muhammad Mera ta yi kira ga ‘yan uwa da ke zaman fursuna da su ɗauki zaman a matsayin jarrabawa daga Allah.
Ta yi wannan kiran ne a yayin wata ziyara da ƙungiyar ta kai gidan gyaran hali da ke garin Argungu makon da ya gabata.
Hajiya Mariya Muhammad Mera ta yaba wa ma’aikatan hukumar bisa ga buɗe makarantar Islamiyya da kuma koyon sana’o’in hannu domin koyon sana’o’i daban-daban da za su riƙe bayan kammala wa’adin zaman gidan gyaran halin.
Hajiya Mariya ta kuma shawarce su da su yi amfani da ilmin da suka koya na addini da sana’o’i da suka koya wajen gyara halayensu.
Da yake jawabi, Muƙaddashin Shugaban hukumar gyaran hali mai kula da wannan gidan idan, ya yaba wa shugabanni da mambobin wannan ƙungiyar bisa ga ɗawainiyar da su ke yi wa mutanen da a ke tsare da su, wanda wannan gaskiya ba ƙaramin karramawa ba ne, inji shi.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta hannanta kyautar Al’ƙuranai a matsayin sadaka don cigaba da karatu a Islamiyya da ke cikin gidan gyaran halin yayin da ita kuma hukumar gidan gyaran halin ta bai wa ƙungiyar kyautar waɗansu kaya da suka haɗa da jakunan hannu da mafifitai (faifai) da ake saƙawa a ɓangaren koyon sana’o’in hannu a gidan.
