ADC ta kori mutumin da ya yi iƙirarin zama shugabanta na ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar ƙawancen ’yan adawa ta ADC a Jihar Gombe sanar da korar mutumin nan da ya yi iƙirarin zama sabon shugabanta na ƙasa, Nafiu Bala, daga jam’iyyar gabaɗaya.

Kazalika, jam’iyyar ta kuma ladabtar da wasu manyan jiga-jiganta su uku, bayan zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa manufar jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Malam Auwal Abba Barde ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Gombe ranar Alhamis.

Ya ce an kori Nafiu Bala daga jam’iyyar ne bayan ya ayyana kansa a matsayin shugabanta na ƙasa tare da sauke wasu mutum uku daga muƙamansu.

Waɗanda aka sauke ɗin a cewar shugaban sun haɗa da Mataimakin Shugaban jam’iyyar na Jiha, Nasiru Lawan da Sakatarenta, Danladi Ya’u da kuma Shugaban Matasa, Abdulkadir Sa’idu Digiri.

Barde ya ce sun gayyaci Nafi’u ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na Nasarawo domin kare kansa amma ya ƙi amsa kiran, wanda hakan ne ya sa aka same shi da laifin rashin da’a ga jam’iyyar.

Ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta lamunci cin amanar jam’iyya ko rashin biyayya ba, tare da tabbatar da cewa ADC ta ci gaba da samun haɗin kai yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

A farkon watan Yuli ne dai gamayyar haɗakar ’yan adawa a Nijeriya suk rungumi jam’iyyar ADC sannan suka ayyana tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Daɓid Mark a matsayin shugaban riƙo na ƙasa.

Kazalika, jam’iyyar ta zaɓi tsohon Gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatarenta na ƙasa.

By ukarofi