Gwamnatin Tarayya ta rufe shafukan sada zamunta miliyan 13.5 saboda karya ƙa’ida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta rufe aƙalla shafukan sada zumunta na ‘yan Nujeriya 13,597,057 saboda yaɗa bayanan da ba su dace ba da kuma karya aa’idar amfani da soshiyal midiya.

An ruwaito cewa sama da ‘yan Nijeriya miliyan 13 sun rasa shafukansu na TikTok, Facebook, Instagram da X (tsohuwar Twitter).

A wata sanarwa da daraktar hulɗa da jama’a na NITDA, Hajiya Hadiza Umar, ta fitar a ranar Laraba, gwamnati ta ce an goge wallafe wallafe 58,909,112 daga shafuka daban-daban saboda karya doka.

Wannan mataki na gwamnati ya fito ne daga rahoton bin Dokar CoP ta 2024 da masu gudanar da dandalan sadarwa irin su Google, Microsoft, da TikTok suka miƙa wa gwamnati.

An fitar da dokar CoP ne bisa haɗin gwiwar Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Nijeriya (NITDA), da Hukumar Yaɗa Labarai ta ƙasa (NBC).

Rahoton na 2024 ya bayyana yadda kafofin sada zumunta ke ƙoƙarin kare jama’a daga illolin amfani da intanet.

Hajiya Hadiza Umar, wadda ta yaba wa Google, Microsoft da TikTok kan ci gaba da bin ƙa’idar amfani da dandalan sadarwa, ta kuma bayyana cewa an shigar da ƙorafe-ƙorafe 754,629 na shafuka ko abin da suka wallafa.

Ta ƙara da cewa, an goge wallafe wallafe 420,439 da ake ganin sun saba da ƙa’ida, amma daga baya aka sake ɗora su a shafukan sakamakon ƙorafin da mawallafan suka yi.

“Rahotannin bin ƙa’idar suna bayar da muhimman bayanai kan yadda shafukan sada zumunta ke ƙoƙarin magance matsalolin tsaro ga masu amfani da su, bisa ƙa’ida da dokokin al’umma na waɗannan kafafen.

“Miƙa wa gwamnati waɗannan rahotannin na nuna wani gagarumin mataki wajen samar da ingantacce da kuma amintaccen yanayi na amfani da yanar gizo ga ‘yan Nijeriya.”

Ta ƙara da cewa, “Hakan na nuna jajircewar waɗannan shafukan sada zumuntar wajen tabbatar da tsaro da amincewar jama’a a yanar gizo.”

Daraktar ta ce, wannan na zuwa ne bayan dokar da ta wajabta wa manyan shafukan sadarwa yin rijista a Nijeriya tare da bin dokokin ƙasar, ciki har da biyan haraji, yayin da ake ƙarfafa tsaro a yanar gizo ga ‘yan ƙasar.

“Yayin da NITDA ta yaba da waɗannan ƙoƙari, muna jaddada cewa samar da ingantaccen yanayi na amfani da yanar gizo na buƙatar haɗin kai na tsakanin duk masu ruwa da tsaki.

“Za mu ci gaba da aiki tare da masana’antu, ƙungiyoyin farar hula da hukumomi don ƙara inganta matakan tsaro, haɓaka ilimin amfani da yanar gizo, da kuma bunƙasa amincewa da gaskiya a cikin tsarin fasahar zamani na Nijeriya,” inji Hajiya Hadiza Umar.

By ukarofi