Lookman ya koma atisaye da Atalanta bayan rushewar shirin komawa Inter Milan

Spread the love

Dan wasan Nijeriya na tawagar Super Eagles Ademola Lookman ya koma atasaye tare da ƙungiyarsa Atalanta, bayan rushewar tattaunawa tsakanin ƙungiyar da Inter Milan kan sauyin sheƙar ɗan wasan.

Kafin yi wa Atalanta kome dai, sai da Lookman ya yi ƙoƙarin tilasta wa ƙungiyarsa tasa amincewa ya koma Inter ta hanyar ƙauracewa zuwa atasaye, har ma da tattara wasu ’yan komatsansa ya kwashe daga ɗakin ajiyar kayayyakin ’yan wasa.

Sai dai haƙar ɗan wasan na Nijeriya ba ta cimma ruwa ba, saboda a ranar Litinin da ta gabata tattaunawa takanin Atalanta da Inter Milan ta watse ba tare da an cimma matsaya ba.

Hakan ta sanya a ranar Talata, Lookman ya lallaɓa ya koma filin atasaye tare da rakiyar mahaifinsa da wani amininsa, nan take kuma ya fara motsa jiki kafin daga bisani ya koma cikin sauran ‘yan wasan Atalanta.

By ukarofi