
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Buratai ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta zaɓi salon kulle da aka yi amfani da shi a lokacin annobar COVID-19 domin daƙile ayyukan ta’addanci, ƴan bindiga da garkuwa da mutane a Nijeriya.
Da yake jawabi a gidan talabijin na Sunrise Daily ranar Juma’a, Buratai ya ce ƙyale ayyukan ta’addanci su cigaba da wanzuwa abu ne mai haɗari ga Nijeriya da al’ummarta don haka akwai buƙatar a ɗauki matakin da ya dace wajen magancewa.
“Za mu iya rufe ƙasar domin tabbatar da kowa ya mayar da hankali kuma a magance waɗannan ɓata garin da ake kira da ƴan ta’adda, ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da dai sauransu”, inji shi.
Ya bayyana cewa, dawo da zaman lafiya a yankunan ƙasar abu ne da ke da buƙatar gudunmuwa daga ƴan siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini gami da ɗaiɗaikun mutane.
A cewarsa, hakan shi ne abinda zai taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa ga rashin tsaron da aka ɗauki tsawon lokaci ana fama da shi a ƙasar.
Ya kuma bada misali da ambaliyar Maiduguri da ta auku bara, inda ya ce daga ko’ina a faɗin ƙasar an kai wa mutanen da lamarin ya shafa ɗauki da tallafi, salon da amfani da irinsa ka iya taimaka wa magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
Buratai ya bayyana ra’ayin nasa ne a lokacin da kiraye-kiraye kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci suka yawaita daga al’umma duba da yadda al’amarin ke ƙamari a sassa daban-daban na ƙasar.
