Jagoran Boko Haram, Bakoura ya musanta mutuwa a harin sojoji ta sama a Nijar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ibrahim Mahamadou Bakoura, wanda jagora ne na mayaƙan Boko Haram da aka sani da Abu Oumaima ya musanta yana ɗaya daga cikin waɗanda aka halaka a farmakin sojoji.

A ranar 15 ga watan Agusta, 2025 rundunar sojoji ta yi ikirarin kashe Bakoura, wanda kuma daɗaɗɗen jagoran ƙungiyar ne na yankin Tsibirin Shilawa dake Kudu maso Gabashin Nijar.

Farmakin sojojin ya hari musamman manyan dabobin mayaƙan a yankunan Korongol, Kournawa da Shilawa da ke shiyyar Diffa.

A yayin harin ne aka halaka da dama daga cikin mayaƙan, wanda aka ƙaddamar ta sama a yankin da Bakoura ke jagoranta.

Saidai, wasu muryoyi daga jami’an tsaro sun shaida cewa jagoran mayaƙan ya musanta batun da ke cewa ya rasu a farmakin.

Mai sharhi akan lamuran daƙile ta’addanci a Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya ce an jiyo Bakoura yana faɗa wa kwamandojinsa cewa ya karanta rahoton da ke cewa ya rasu a Soshiyal Mediya, kamar yadda Jamhuriyar Nijar ta sanar.

Mahamadou ya shiga Boko Haram ne shekaru 13 da suka gabata, inda ya kuma karɓi jagorancin ƙungiyar bayan rasuwar tsohon shugabanta, Aboubacar Shekau.

By Babaji