Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamandan rundunar kula da haƙo ma’adanai ta Mining Marshals, John Onoja Attah, ya ce haƙo ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na barazana ga tattalin arzikin Nijeriya, muhalli da tsaron ƙasa.
Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa reshen Abuja ta shirya a Abuja, inda ya bayyana cewa Nijeriya ta yi asarar biliyoyin kuɗaɗe sakamakon haƙo ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, baya ga lalacewar gonaki da tashin hankali a al’ummomi.
Attah ya ce rundunar ta Mining Marshals, ƙarƙashin hukumar NSCDC, an kafa su ne da umarnin Shugaba Bola Tinubu da Ministan ma’adinai, Dele Alake, domin dawo da doka a fannin ma’adinai.
Ya bayyana cewa rundunar ta rusa sansanonin masu haƙar ma’adinai, ta kama da gurfanar da masu laifi, tare da dawo da zaman lafiya a wasu yankuna.
Haka kuma, an farfaɗo da dokar Minerals and Mining Act 2007 da Mining Regulations 2011, inda ake iya ɗaure masu safarar ma’adinai ba tare da rajista ba har abada.
Kwamandan ya roƙi ‘yan jarida da su kasance abokan haɗin gwiwa wajen yaƙar wannan ɓarna, tare da yin watsi da rahotannin ƙarya da ake yaɗawa don ɓata sunan rundunar.
Shugabar ƙungiyar ‘yan jaridu ta Abuja Grace Ike, ta tabbatar da cewa za su ci gaba da ƙarfafa ƙwararru a aikin jarida, yayin da shugaban ƙungiyar masu haƙar ma’adinai, Dele Ayanleke, ya ce aikin rundunar ya dawo da ƙwarin gwiwar masu saka hannun jari na gaskiya.
