
Yayin da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya shawarci ƴan Nijeriya da su ɗauki matakin koyon kare kai don tsira daga sharin ƴan ta’adda, kalaman nasa sun haddasa cecekuce acikin al’umma musamman a harkokin tsaro, shari’a, ƴancin jinsi da rayuwar yau da kullum.
Janar Musa ya bayyana cewa sanin yadda mutum zai kare kansa abu ne mai muhimmanci kamar yadda koyon tuƙi da iyo suke a wajen ɗan-adam.
Matar tsohon gwamna a Jihar Ondo , Betty Anyanwu-Akeredolu, ta goyi bayan kalaman babban hafsan inda ta ce ta jima da da buɗe wajen koyon horon faɗan ‘taekwondo’ ga ƴan mata tun a shekarar 2017, saboda matsalolin fyaɗe da cin zarafi, kamar yadda ta bayyana ta kafar X.
Saidai, wasu sun fassara kalaman babban hafsan da ma’anar a ɗauki makami ko kuma a ɗauki doka a hannu a yayin fuskantar ta’addanci.
Hedikwatar Tsaro DHQ, ta yi karin haske game da kiran inda ta ce, jama’a sun yi mai wata fahimta ta daban, to amma abin da babban jami’in tsaron ke nufin shi ne ba wai mutane su ɗauki makami su kare kansu ba, a’a yana nufin su koyi abubuwa kamar kokowa da judo da dambe da ninƙaya da gudu da tuƙin mota da dai sauransu.
Birgediya Janar Tukur Gusau, shi ne daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya, ya shaida wa BBC cewa shi babban hafsan tsaron na nufin cewa a matsayinka na adam bai kamata ka zauna haka kawai ba tare da ka koyi wata dabara da za a kare kanka ba.
Ya ce,” A misali irin mutanen nan da ketare mutane suna kwace musu waya da yawansu wasunsu basa dauke da makami karfi kawai suke nuna wa jama’a, to irin wannan yanayi ne shi babban hafsan tsaron ke ganin ya kamata mutane su koyi dabarun kansu kamar kokawa da gudu, inda duk wanda ya nuna maka karfi kai ma sai ka ware gwanjinka.”
“Maganar a dauki makami ma dokoki na Najeriya ma basu yadda wanda ba shi da hurumin daukar makami su dauka ba, idan kuwa har suka dauki makami to akwai dokar da zata yi aiki a kansu.”In ji Janar Tukur Gusau.
