Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) ya miƙa saƙon ta’aziyya da jajantawa akan hare-haren da ‘yan bindiga su ka kai a wani masallaci da ke ƙauyen Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi wanda yayi sanadiyar rasa rayuka da dama.
“A madadin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Katsina ina miƙa saƙon ta’aziyya da jajantawa ga al-ummar Unguwar Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi bisa iftila’in da ya faru na harin da yan bindiga su ka kai wanda yayi sanadiyar rasa rayuka da jikkata wasu,”inji Sheikh Yakubu Musa.
Ya roƙi Allah (S.W.A) ya jiƙan waɗanda su ka rasu, ya gafarta masu ya ba iyalai da yan’uwa haƙurin rashin su. Su kuma waɗanda su ka samu raunuka Allah ya ba su lafiya.
Sai yayi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta ƙara ƙoƙari a kan wanda ta ke yi kan matsalar tsaro domin yanzu a wasu sassan jihar ana zaman ɗar-ɗar da fargaba na yiwuwar kai hare hare na ƴan bindigan.
“Kaman yadda muka gani bayan faruwar lamarin muƙaddashin gwamnan yayi kira da roƙo ga shugaban ƙasa da ya dubi halin da al’ummar Katsina su ke ciki, ya kawo masu ɗauki game da wannan babbar barazanar ta matsalar tsaro da ke damun wasu sassan jihar abin a yaba ne.
Haka kuma yadda mu ka ji muƙaddashin gwamnan ya haɗu da hafsan sojojin Najeriya a Abuja jiya kan matsalar tsaron inda ya bayyana irin illar da matsalar tsaro ke yi ga rayuwar al’ummomin karkara, musamman asarar rayuka, dukiya da kuma rushewar harkokin noma a jihar.
Muna kira da a cigaba da matsa masu lamba har sai an tabbatar da sun yi abinda ya dace game da wannan matsala domin al’ummar Jihar Katsina su na buƙatar rayuwa cikin aminci saboda haka muna ƙara kira ga gwamnatin Jihar Katsina ta ƙara ƙoƙari kan wanda ta ke yi kan wannan matsala
Shugaban izalan kuma ya ƙara kira ga limamai da malamai akan sanya wannan matsala cikin addu’a a duk lokuttan da aka gabatar da ibada ko ayyukan alkhairi domin yin tawassali da su wajen roƙon Allah ya kawo ƙarshen wannan matsala.
“Haka su ma sauran al-umma akwai nauyin da ya rataya akan su na gudummuwar da za su bada domin magance wannan matsala tun daga addu’a, aikin sa kai domin kare garuruwansu ,”Sheikh Yakubu Musa ya ce.
Ya yi roƙon Allah (S.W.A) ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ƙasa baki ɗaya.
