Hedikwatar Tsaro ta ƙi amincewa da yadda aka fassara kalaman Janar Musa kan kare kai

Spread the love

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta yi karin haske game da kiran da Babban Hafsan Tsaro Janar Christopher Musa ya yi cewa jama’a su fara tunanin koyon dabarun kare kansu da aka amince da su a duk faɗin duniya.

Ta ce, jama’a sun yi wa kiran wata fahimta ta daban, to amma abin da babban jami’in tsaron ke nufin shi ne ba wai mutane su dauki makami su kare kansu ba, a’a yana nufin su koyi abubuwa kamar kokowa da judo da dambe da ninkaya da gudu dama tukin mota da dai sauransu.

Daraktan yaɗa labaran DHQ, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa shi babban hafsan tsaron na nufin cewa a matsayinka na adam bai kamata ka zauna haka kawai ba tare da ka koyi wata dabara da za a kare kanka ba.

Ya ce,” A misali irin mutanen nan da ketare mutane suna kwace musu waya da yawansu wasunsu basa dauke da makami karfi kawai suke nuna wa jama’a, to irin wannan yanayi ne shi babban hafsan tsaron ke ganin ya kamata mutane su koyi dabarun kansu kamar kokawa da gudu, inda duk wanda ya nuna maka karfi kai ma sai ka ware gwanjinka.”

“Maganar a ɗauki makami ma dokoki na Najeriya ma ba su yadda wanda ba shi da hurumin daukar makami su dauka ba, idan kuwa har suka dauki makami to akwai dokar da zata yi aiki a kansu”, inji Janar Tukur Gusau.

By Babaji