Yanzu-yanzu: Tinubu ya dawo Nijeriya bayan tafiyar kwana 12 zuwa Japan da Brazil

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar tarukan harkokin ci-gaba tsakanin shugabannin ƙasashe a Japan da Brazil.

Shugaban ƙasar ya dawo ne a safiyar yau Alhamis, 28 ga Agusta, 2025, kamar yadda Kakakinsa, Bayo Onanuga ya faɗa a wata takarda.

Ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Nuhu Ribadu (NSA); Gwamnan Imo, Hope Uzodimma da sauransu.

A ranar 20 ga watan nan na Agusta Tinubu ya halarci babban taron Ci-gaban Afirka a Tokyo karo na tara (TICAD9) a Japan.

Ya tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi ci-gaba ciki har da wasu manyan jami’an gwamnatin Nijeriya.

Baya ga ficewarsa daga ƙasar, sai ya yada zango a birnin Los Angeles gabannin tafiya Brasilia inda ya gana da Shugaba Inacio Da Silva da wasu manyan jami’an gwamnatin Brazil.

By Babaji