2027: Jonathan bai tsame kansa daga tsaya wa takara ba, inji ɗan uwansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya musanta rahotannin da ke cewa ya jingine shirinsa na tsaya wa takara a zaɓen 2027, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.

Hakan na zuwa ne a lokacin da wani rahoto da jaridar ‘Newsweek Nigeria’ ta wallafa ya nuna cewa Jonathan ya janye batun tsaya wa takara domin kada ya samar da rarrabuwar kai a kudanci yayin zaɓen 2027.

Duk da cewa tsohon shugaban ƙasar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, alamu masu ƙarfi na nuna akwai yiwuwar ya shiga sahun masu neman kujerar shugaban ƙasa a 2027 yayin da ake cigaba da tattaunawa da masu ruwa tsaki a faɗin ƙasar.

A yau Juma’a ɗan uwa ga Jonathan, Aziboala Robert ya ƙaryata rahoton batun janyewar tsohon shugaban ƙasar a shafinsa na Facebook, inda ya ce Jonathan bai taɓa cewa ba zai tsaya takara ba a 2027.

Ya bayyana rahoton a matsayin zancen ƙarya da ake ƙoƙarin ruɗar da tunanin al’umma da shi, yana mai kira da a yi watsi da shi.

Jonathan, wanda ya shugabanci Nijeriya daga 2010 zuwa 2015 yana ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴan siyasar da suka yi fice a ƙasar, wanda tsayawarsa takarar shugaban ƙasa daga kudu za ta yi tsari sosai ga zaɓen 2027.

By Babaji