Tsohon GM na Marshall, Haruna Jonga ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jam’iyyar APC a Jihar Gombe ta yi babban kamu, bayan da tsohon Janar Manajan hukumar tsaro ta Marshall da gwamnatin da ta gabata ta kafa, Alhaji Haruna Jonga, ya fice daga PDP tare da rattaba hannu kan takardar shigarsa jam’iyya mai mulki ta APC.

Taron tarbar sa ya gudana a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe, inda shugaban ƙaramar hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana cewa shigowar Jonga APC babban alheri ne da ke tabbatar da irin amincewar al’umma ga ayyukan ci gaban Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Ya ce:“Shigowar Jonga APC ya nuna yadda Gwamna Inuwa Yahaya ya cirewa Gombawa kitse daga wuta. Wannan ƙarin ƙwarin gwiwa ne a gare mu wajen tabbatar da nasarar jam’iyya a gaba.”

Barista. Sani, wanda shi ne shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na Gombe (ALGON), ya ƙara da cewa wannan sauya sheka ya nuna alamar cewa APC za ta ci gaba da riƙe madafun iko a Gombe har bayan 2027.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, ya bayyana farin cikinsa da ƙarin goyon bayan da Jonga ya kawo wa jam’iyyar.

“Mun samu ƙarin kwamandan yaƙi wanda PDP ke alfahari da shi a baya. Yanzu dai mun zama ɗaya, babu wanda ya fi wani, sai dai mu ci gaba da yiwa jam’iyya aiki domin sake samun nasara a 2027.” inji Danladi

Da yake bayyana dalilansa na sauya sheka, Alhaji Haruna Jonga ya bayyana cewa babban abin da ya jawo shi APC shi ne dimbin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Inuwa Yahaya ke gudanarwa a faɗin Jihar Gombe.

Duk mai kishin Gombe dole ya tsaya a layin Gwamna Inuwa Yahaya domin ci gaban jihar ya zauna a zuciyarsa,” in ji shi.

By ukarofi