
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta fallasa wata dabar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke ayyukansu a fannin sufurin jiragen sama na Nijeriya.
Ta kuma zarge su da sanya ababen maye a kayan maniyyatan aikin hajji ko umara domin jefa su a matsala yayin da suka isa ƙasashen waje.
NDLEA ta fitar da rahoton ne kwanaki kaɗan da hukumomin Saudiyya suka tsare wasu masu umara daga Nijeriya da suka haɗa da Maryam Hussaini Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da kuma Abdulhamid Sadiq bisa zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi.
Lamarin da ya jefa fannin sufurin jiragen sama na Nijeriya cikin firgici duba da kiraye-kirayen da yake samu daga wurare da dama akan batun.
Daraktan yaɗa labaran NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa wani jirgin sama na Ethiopian Airlines ya tashi daga Kano zuwa Jidda a ranar 6 ga wannan watan na Agusta, inda aka gano cewa yana ɗauke da ƙarin wasu jakukkuna guda shida da wasu gurɓatattun ma’aikata da aka haɗa baki da su suka sanya su acikinsa.
An yi nasarar kama guda uku daga ciki a Jidda waɗanda ke ƙarƙashin mutane ukun da aka kama, inda aka gano suna ɗauke da wasu miyagun ƙwayoyi.
Akan haka ne hukumomin Saudiyyan suka tsare su duk da cewa shaidu sun nuna cewa ba su da laifi a kai.
Masu bincike na NDLEA sun gano cewa wani mai suna Mohammed Ali Abubakar mai shekaru 55 da aka sani da Bello Karama ke da alhakin ƙulla makircin da wani ma’aikacin Kamfanin Skyway Aviation Handling (SAHCO).
Abubakar shi ne wanda ya yi kutsen ƙwayoyin a Ethiopian Airlines inda ya fice zuwa Jidda a ranar ta Egypt Air, domin kauce wa zargi.
