Amurka ta ƙi bai wa wakilan Palesɗinu biza gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta tabattar da soke bizar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wasu jami’an Falasɗinawa su guda 80.

Wannan mataki dai zai hana Mahamoud Abbas halatar taron ƙoli na MƊD da za a yi a watan Gobe a birnin Washington na Amurka.

A taron ne dai aka yi tunanin ƙasashe da dama sun ƙudiri anniyar amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci, wanda shi ne babban burin mutanen yankin.

Isra’ila ta dage kai da fata cewa bai kamata a ba Falasɗinu ƴancin zama cikakkiyar ƙasa ba, kuma tana samun goyon bayan Amurka, kamar yadda BBC Hausa taruwaito.

By Babaji