2027: Jonathan ba zai iya kada Tinubu ba – APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC a Jihar Legas ta ce ta fahimci akwai yiwuwar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya tsaya takara a zaɓen 2027 da ke tafe.

Rahotanni sun bayyana cewa, Jonathan wanda ya rasa damar koma wa karagar mulki a 2015 a karo na biyu, na samun kira daga magoya bayansa na ya sake fitowa takara a wannan karo.

Da yake magana a wata takarda ranar Juma’a, Kakakin jam’iyyar a Legas, Seye Oladejo ya ce abu ne mai wahala a ce tasirin tsohon shugaban ƙasar a siyasance ya iya kada Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa, wa’adin Jonathan na 2010 zuwa 2015 ya bar baya da ƙura a ƙasar inda ya fuskanci matsaloli da dama da suka haifar mata da koma-baya kama daga rashawa zuwa matsanancin rashin tsaro da barazanar tattalin arziƙi.

Kakakin ya ƙara da cewa, shugabanci ƙasar a yanzu abu ne da ke buƙatar jajircewa, cancanta da hangen nesa ba dawowa daga rashin nasara ba.

Kazalika, ya ce jam’iyyar tana sane da ɗaurarrun ababen da dokokin ƙasa da na siyasa suka tanadar akan tsayawarsa takara duba da cewa ya yi sama da wa’adi ɗaya akan kujerar mulki, lamarin da ka iya haddasa tsaiko daga jam’iyya ko shari’a.

By Babaji